Connect with us

WASANNI

Nijeriya Ce Babban Kalubalenmu, Cewar Sadio Mane

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Senegal, Sadio Mane, kuma dan tawagar Liberpool, ya tabbatar da cewa babban kalubalen da yake gabansu a wanann gasar shine haduwa da tawagar Super Eagles ta Nijeriya.

Senegal ta lallasa Benin da kwallo 1-0 mai ban haushi, duk dai a wasannin gasar cin kofin Afrikan da yake gudana a Masar kuma yayin buga wasan tsakanin Benin da Senegal an yi ta fafatawa har zuwa dawowa daga hutun rabin lokaci ba tare da wani bangare ya yi nasara ba, kafin daga bisani, Idrissa Gana Gueye, dan Eberton ya zurawa Senegal kwallonta daya tal a minti na 70 da fara wasa.

Su ma dai yayin wasan na su a bangren Benin ‘yan wasan irinsu Cebio Soukou da Stebe Mounie sun samu katin gargadi, yayinda Oliber Berdon kuma ya samu jan kati dungurugum, a bangaren Senegal kuma dan wasan gaba na Liberpool Sadio Mane ya samu na shi katin gargadin.

“Muna da tawaga mai kyau kuma mai karfi sai dai kuma duk da haka akwai manyan kasashe banda Nijeriya wadanda zamu niya haduwa dasu kuma su bamu babbar matsala amma dai yanzu babu kamar Nijeriya” in ji Mane

Ya cigaba da cewa “Babban abinda yake gabansu shine samun nasara a ragowar wasannin da suke gabansu musamman wasan da zasu buga na kusa dana karshe wanda daga nan ne kuma zasu samu zuwa matakin wasan karshe.

A karshe Mane ya bayyana cewa gasar da ake bugawa ta wannan shekarar tana kayatarwa saboda manya manyan kasashe sun samu halartar gasar sannan kuma shahararrun ‘yan wasa sun samu zuwa gasar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: