Connect with us

WASANNI

Origi Ya Sake Sabunta Kwantiragi Da Liverpool

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Dibock Origi, ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya bayan taimakawa kungiyar lashe gasar Zakarun Tiurai a kakar wasan data gabata kuma suka kammala gasar firimiya a mataki na biyu.

Dan kwallon na Belgium mai shekara 24, ya koma Liverpool ne daga kungiyar kwallon kafa ta Lille dake kasar Faransa  a shekara ta 2014 amma ya shafe shekara biyu a matsayin aro a kungiyoyi da dama.

Sai dai ya taka rawar gani bayan ya dawo a bara, inda ya zura kwallo biyu a wasansu da Barcelona sannan ya ci kwallo ta biyu a wasan karshe su da Tottenham kuma suka zamo zakara karo na bakwai a tarihi.

“Na dade ina jin cewa ina so na ci gaba da zama a Liverpool saboda akwai wani abu na musamman tattare da zama a wannan kungiya saboda haka ina farin ciki damar da wanann kungiya ta sake bani” in ji Origi

Ya cigaba da cewa “Babban burina shine ganin a kakar wasa mai zuwa mun lashe gasar cin kofin firimiya saboda shine burin kowanne dan wasa a Liverpool kuma yadda muka shirya tabbas abune wanda zai iya kasancewa”

Har yanzu dai Liverpool bata sayi dan wasa ko daya ba a kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta wannan shekarar kuma tuni kungiyar ta saki ‘yan wasa irinsu Alberto Moreno da kuma Daniel Sturidge.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!