Connect with us

WASANNI

Sakon Buhari Ga Super Eagles: Burinmu Ku Kawo Mana Kofi Gida

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa ‘yan wasan kasar nan kan rawar da take takawa a gasar cin kofin kasashen Afirka da ake yi a Masar bayan da a ranar Laraba ne Super Eagles ta kai zagayen kusa da na karshe bayan da ta doke Afirka ta Kudu da ci 2-1.

Kwallon da William Troost-Ekong ya zura ana dab da tashi ita ce ta bai wa Nijeriya wannan damar kuma ta doke kasar ta Africa ta Kudu wadda ta doke kasar Masar, wato mai masaukin baki a ranar Asabar din data gabata

A sakon da ya wallafa a shafinsa na sadarwa na Twitter, shugaban ya taya ‘yan Super Eagles murna, yana mai cewa ‘yan kasar sun kagu su ga tawagar ta lashe wasa biyu nan gaba domin kawo kofin gida Nijeriya.

Matashin dan wasa Samuel Chukwueze ne ya fara zura kwallo a ragar Bafana Bafana bayan da Aled Iwobi ya bugo masa kwallo sai dai kuma daga baya  Bongani Zungu ya ramawa Afirka ta Kudu  kwallon wadda da farko aka soke saboda zargin satar gida amma daga baya na’urar da ke tallafa wa alkalin wasa ta ce babu satar gida, abin da ya sa aka amshi kwallon.

Sai dai dan wasan baya na Udinese Troost-Ekong ya samu nasarar jefa kwallo a raga ana dab da kammala wasa, wacce kuma ita ce ta raba gardama sai dai ya ci kwallon ne cikin sauki bayan da kwallon da Moses Simon ya bugo ta kufcewa mai tsaron ragar Afirka ta Kudu Ronwen Williams.

Nijeriya za ta kara da Ibory Coast ko Algeria a wasan kusa da na karshe da za a buga ranar Lahadi da misalin karfe (8.00) na dare a gogon Nijeriya da Nijar kuma duk kasar data samu nasara zata tsallaka zuwa wasan karshe.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: