Connect with us

LABARAI

Sana’ar Gwangwan: Matashi Dan Arewa Ya Sami Rufin Asiri Mai Yawa A Legas

Published

on

Alhaji Salisu Abdullahi Umar Tafidan Gatankowa da ke Oke-odo a birnin Lagas ya bayyana rufin asirin da ke cikin sana’a ta gwangwan domin matasa masu sha’awar sana’ar su samu qwarin gwiwar kamawa.

Ya bayyana haka ne ga wakilin LEADERSHIP A YAU JUMA’A a Legas, inda ya bayyana cewa sailin da suka fara sana’ar, suna yawo ne cikin bola suna tsintar qarafuna da robobi.

Ya qara da cewa sa’ilin da ya fara yana dan shekara ashirin da biyar da haihuwa a duniya, bayan ya gama makarantarsa ta polytechnic a Kano yana da takardarsa ta Difiloma.

Ko da ya ga bai sami aikin yi ba, kawai sai ya shiga wannan harkar ta neman karafuna yana kawowa a saya, har ya dawo shi ma in an kawo su saya.

Alhaji Salisu Abdullahi Umar Tafidan Gatankowa ya qara da cewa yanzu har ya kai suna hulda da kamfaninnika, inda yaka da ma’aikata da suke aiki a karkashinsa dari uku.

Sai dai, kafin yakai wannan matsayi ya zauna a qarqashin Yarabawa suka koya masa wannan kasuwanci, wani lokaci a biya su, wani lokaci ba za a biya su ba, amma kasancewar akwai abin da suka sa a gaba, haka suka yi ta hakuri har suka samu nasara, kana ya bayyana cewa yanzu haka akwai wasu daga cikin ‘ya’yan Yarabawan da suka koya masa sana’ar a hannunsa shi ma yana koyar da su. Wannan kuma a cewarsa ya samu ne saboda irin biyayyar da ya yi wa iyayensu.

Don haka, ya yi kira ga matasa su rungumi koyon sana’a, yana mai qarawa da cewa, “matasa ku yi hakuri kuma ku yi biyayya a duk inda kuke koyon sana’a”.

Alhaji Salisu Abdullahi Umar Tafidan Gatankowa ya roqi gwamnati da ta tallafa masu domin su ma suna rage yawan datti a muhallin qasa, wanda kowa ya san tsaftar muhalli na da matuqar muhimmanci wurin kiwon lafiyar ‘yan qasa.

Ya kuma yi kira ga iyayen yara su horar dasu dogaro da kai, kana ya nemi ‘yan arewa mazauna Lagas su yi qara daura damara kan dagewa wajen neman abin da zai amfanesu, kana ya yi wa Nijeriya fatan alkhairi da Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-olu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: