Connect with us

RAHOTANNI

Sarkin Minna Ya Yaba Wa Gwamnan Neja Kan Zaben Jami’ar Yada Labaran Gwamna

Published

on

Mai Martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Faruk Bahago, ya yabawa gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, kan zaben Mary Noel Berje, a matsayin sabuwar jami’ar yada labaran gwamna domin yin aiki kafada da kafada da gwamnan don ganin an gudanar da harkokin gwamnati yadda ya kamata.

Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da sabuwar jami’ar yada labaran gwamna ta ziyarce shi a fadar sa da ke Minna.

Mai Martaba ya ce, gwamnan ya ba ta wannan matsayin ne bisa cancanta da dacewarta a matsayin mace ta farko da ta samu damar rike wannan matsayin, don haka ya jawo hankalin gwamnati da ta bada damar yin aiki yadda ya kamata ta hanyar tallafa ma ta yadda aikin zai tafi yadda ya da ce.

Ya jawo hankalin sabuwar jami’ar da ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta gudanar da aiki yadda ya kamata kamar yadda ake cewa komai namiji ya yi mace ma za ta iya, ta tabbatar ta nuna kwarewa da bajinta ta yadda za ta zama abin alfahari ga wanda ya kawo ta don tallafa masa.

Dakta Umar Faruk Bahago, ya ce gwamnatin Alhaji Abubakar Sani Bello gwamnati ce da ta himmantu wajen farfado da tattalin arziki, don haka jama’a mu baiwa gwamnati goyon baya da hadin kai don ganin ta cimma manufofinta na samar da ci gaban jihar.

Mai Martaba Sarki, ya roki Allah Subhanahu da ya taimaki jami’ar yada labaran da gwamnatin jiha da ya nuna masu hanya da taimakon su don samun nasarar ayyukan alherin da suka sanya a gaba wajen ganin sun sauke nauyin da aka dora masu.

Da take jawabi a gaban Mai Martaba ta ce, ta zo don neman albarkar sa a matsayinsa na uba don samun nasarar aikin da aka dora mata.

Mary Berje ta sha alwashin yin aiki yadda ya kamata ta hanyar bude kofa ga kowa kamar yadda tsarin gwamna Abubakar Sani Bello yake gudana don ganin gwamnan ya samu nasarar inganta tattalin arzikin jihar wanda ake fatar bunkasa jihar da shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: