Connect with us

LABARAI

Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa: An Kai Wa Shaidun PDP Hari

Published

on

Zaman kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasar Nijeriya ya fuskanci tsaiko a wannan Juma’ar, bayan da lauyoyin jam’iyyar PDP da na dan takararta Atiku Abubakar suka ce harin ‘yan bindiga ya rutsa da wasu shaidun da suke shirin gabatarwa, a gaban kotun don kalubalantar sakamkon zaben 23 ga watan Fabrairun shekarar 2019.

Daya daga cikin lauyoyin masu gabatar da karar Chris Uche SAN, yace sun gayyaci shaidu 8 ne a wannan Juma’a domin bada bayani kan abinda suka sani na zargin tafka magudi a zaben shugaban kasar da ya gabata.

Lauyan ya ce a lokacin da lamarin ya auku, shaidun nasu na kan hanyar zuwa Abuja ne daga jihar Zamfara. Ana sa ran cewa kotun sauraron kararrakin zaben shugabancin na Nijeriya karkashin jagorancin mai shari’a Muhammed Garba za ta ci gaba da zama a makon gobe, lokacin da shaidun da PDP ke gabatarwa za su cika 36, kamar yadda lauyoyin masu kara suka nema.

A nasu bangaren lauyoyin masu kare wadanda ake kara sun bukaci kotun ta yi watsi da bukatar lauyoyin PDP da dan takararta na dage zaman zuwa mako mai zuwa
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!