Connect with us

WASIKU

‘Shugaban Kasa Ka Darje Ministoci Masu Kima A Idon Jama’a’

Published

on

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. Hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar kasa. Muna muku addu’ar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jini baki daya. Ina kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kula sosai wajen zaban ministocinsa. Domin kar a maimaita abun da ya faru a karon mulkinsa na farko, ga shi ya dade kafin ya fitar da sunayen ministocin, amma kuma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Duk wata gwamnati mai mulki tana samun nasarar ce, idan ta samu wazirai masu daraja a idon jama’a. Mana mutane na kwai wanda za su yi aikinsu tsakani da Allah tare da son zuciya ba. Lallai muna bukatar mutane na kwarai a matsayin ministoci wadanda za su taimaka wa wannan gwamnatin wajen share wa talakawa hawayensu. Ina rokon Allah ya taimaka wa shugaban kasa wajen zakulo mutane masu kishin wannan kasa.

Sako daga Muhammad Barista, Kaduna.

08078497517

‘Ya Kamata Gwamnati Ta Dauki Matakin Gaggawa A Kan ‘Yan Shi’a’

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Juma’a. Barkan ku da aiki, ina muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addu’a Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya. Ina kira ga Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dauki matakin gaggawa a kan ‘yan kungiyar shi’a. Abin da ya faru cikin wannan makon, ya nuna cewa akwai bukatar gwamnati ta dauki kwararan matakai da suka dace ga duk masu karya doka a wannan kasa. Sun aikata laifuka a kokarinsu na shiga fadar majalisar tarayya a birnin tarayya Abuja, sun kona motoci, sun lalata kayan gwamnati, kuma sun raunata bayin Allah.

Idan dai har ‘yan shi’ah za su yi yunkurin shiga fadar majalisar tarayya, to wata rana ma fadar shugaban kasa na Aso Rock za su shiga.

Bai kamata gwamnatin shugaba Buhari ta zuba ido abu na faruwa ba tare da daukar kwakkwaran matakin da ya dace ba, ana kashe mana jami’an tsaro, ina jin tsoron ranar da za a ce jami’an tsaro a Abuja sun gaji da abin da ke faruwa tsakaninsu da ‘yan shi’a

Idan gwamnatin Buhari ta gaza wajen daukar matakin da ya dace, to a sakar musu shugabansu kawai, ko hakan zai kawo karshen wutar fitinar da ke kokarin tashi a Nijeriya wanda ba za a iya kashe ta ba.

Dukkan alama ya nuna mana kungiyar shi’a magoya bayan Zakzaky sun yi karfin da ya wuce tunanin duk wani mai tunani, suna da manyan wakilai a cikin gwamnati da suke ba su goyon baya a boye, suna da manyan wakilai a cikin hukumomin tsaron soji, ‘yan sanda, DSS da kuma NIA, suna da wakilai a cikin gwamnoni, fadar majalisar wakilai da sauran manyan ma’aikatu, abin da ya rage musu kawai shi ne, daukar makami wanda ba ma fata a kai ga haka.

Abin da aka karantar damu a bangaren yaki da ayyukan ta’addanci shi ne; akwai bambanci a tsakanin mutanen da suke yaki a kan akida da mutanen da suke yaki a kan neman ‘yanci ko kuma zalunci, masu yaki a kan akida sune mafi wahalar sha’ani wajen magancewa, domin su mutuwar suke nema, ba kamar wadancan da suke yaki a kan neman ‘yanci ko zalunci don su rayu su ji dadin duniya ba.

Hakika shugaba Buhari yana bukatar shawara daga kwararrun masana tsaro, ba mu sani ba ko amanarsa ake ci ana boye masa gaskiyar al’amari, Allah ne kadai Ya sani, amma hakika gwamnatin shugaba Buhari tana yin sakaci a kan wannan lamari.

Sako daga Wani Dan Kishin Kasa

‘Gwamnati Ta Duba Rayuwar Talakawan Nijeriya’

Assalamu alaikum, Editan LEADERSHIP A YAU JUMA’A, ina so ka bani dama na bayyana abin da yake ci min tuwo a kwarya. Abun dubawa ne kwarai yadda talaka ke gudanar da rayuwarsa a wannan kasa ta Nijeya. Ganin yadda rayuwar ke fadawa cikin yanayi na kunci da damuwa, a yau a Nijeriya  har akwai wanda zai kwana a gidansa ba tare da abinci ba.

Ko me ya sa haka? Abun na da matukar kulle kai ganin yadda Nijeriya ke da dimbin arzikin kasa da kuma albarkatun kasa, harma ana sanya ta a jerin kasashe ke da arzikin kasa. Ga kuma tashe-tashen hankula wadanda suka hada da kabilanci, siyasa, dama na addini sun dade suna ruguza lamarin kasar nan, kuma hasashe ya nuna cewa wadannan rigin gimu ba sa rasa nasaba da waccar matsala ta rashin jin dadin rayuwa da talaka ba ya yi, wanda ka iya jefa shi cikin halin rashin tsoron tayar da dukkan wata rigima a kasa.

Ina kira ga wakilan jihohin Nijeriya da wakilan tarayya, sanatocin Nijeriya  gwamnonin Nijeriya da kuma shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari da a yi duba kan rayuwar talakawan kasar nan, a tsoma talakawa cikin ayyukan da za su motsa rayuwar jama’a ta yadda za a samu nasarar gudu tare a kuma tsira tare. Amma gaskiyar magana shi ne, talakawa suna matukar shan wahalar rayuwa a wannan lokaci.

Sako daga Mahmud Sani, KD.

08151693170
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: