Connect with us

MAKALAR YAU

Siyasar Kashin Dankali Da Ake Wa Kudaden Kananan Hukumomi

Published

on

Sama da Zango biyu cikin wannan Jamhuriyar Siyasa ta Hudu a Nijeriya, daukacin Gwamnonin Kasar ke yi wa makudan kudaden Kananan Hukumomi kanshin-mutuwa, baba-kere da kisan-mummuke.

Da Gwamnonin PDP, da na APC, da na APGA, hada da na sauran jam’iyyu, sai suka hada-kai wuriguda tare da zama abokanan cin-mushe a lokaci guda, kasantuwar kwaryar-sama ce ke bugun ta kas, wajen yin kwanciyar migirbi birnishin makudan biliyoyin nairori da ake antayowa cikin daukacin Kananan Hukumomi 774 da ake da su a Kasa, a duk karshen Wata, a matsayin kudin (Statutory Allocation) da Tsarin Mulkin Kasa ya wajabta fitar musu, tamkar yad da suma Jihohi da Gwamnatin Tarayya, tsarin mulkin ya shelanta ware musu nasu kaso.

Waccan sakiyar da babu ruwa da Gwamnonin ke yi wa Kananan Hukumomi, wajen turmushe wadancan kudade na wata-wata, yai sanadiyyar mayar da Satariyoyin Kananan Hukumomi tamkar kufai ko makabartu. Kamar yad da Gwamna yake zababbe a Tsarin Mulki da kundin Dokar Zabe, haka shi ma Ciyaman na karamar hukuma yake, sai dai sakamakon wancan saki-na-dafe da gwamna yai wa ciyaman, sai Shugaban Karamar Hukuma ya koma tamkar kyanwar lami. Ba sawa ba fitarwa. Sai katon Ofis makeke, amma ba fusss! Mhm! Nijeriya kashin-dankali!!!

Wani abu da yake bai wa al’umar Kasa mamaki game da wannan mummunar cin-kwalar kudaden Kananan Hukumomi da daukacin Gwamnonin Kasar ke yi shi ne, babbancin ra’ayin siyasa,  ko na addini, ko na kabila, ko na bangarenci, duka bai kange su ga yin magana da yawu guda ba wajen turmushe kudaden.

Wane lokaci ne a Kasar, Gwamnoni suka hade kai wuriguda, suka kalubalanci Gwamnatin Tarayya, na sai ta tabbatar da ingantacciya kuma isasshiyar wutar lantarki ga “Yan Kasa? Ko yaushe ne, wadannan Gwamnoni, suka matsa lamba da murya guda ga Gwamnatin Tarayya cewa, ta gaggauta kammala gyara da karasa sabbin ayyukan Titunanta na Kasa dake warwatse cikin Jihohi, musamman a wuraren da ake yawan samun asarar rayukan al’umar jihohin nasu? Ko mai karatu ya taba jin Gwamnonin sun tinkari Gwamnatin Tarayya a dunkulen su, sun ce lallai ta tashi ta yi maganin Kanfanonin Sadarwa da ake da su a Kasa, bisa mugun zaluntar al’umar Kasa da suke yi, wajen lakume musu makudan kudadensu dare da rana ta hanyar “yan dabaru da ci-da-ceto? Idan babu gamsassun amsoshi ga wadannan tambayoyi, to me ya sa, sai wajen danne kudaden kananan hukumomi ne suka iya hade kai a yi magana da yawu-guda?.

Wani na iya cewa, ai sun yi taruka da yawu guda a wasu lokuta game da batun tsaro. Toh! Taron shan shayi za a kira shi ko me? Bayan irin wadancan taruka, fitar da wani sakamako guda daya kwakkwara wanda aka samu, sakamakon gamawar tasu! Ba ma haka ba, ka sani cewa, game da batun kananan hukumomi, ba ya ga hade-baki wuriguda, sukan kuma garzaya Kotu ma da yawu guda, duka dai game da yunkurin lashe hakkin da ba nasu ba.

Ashe irin kyalayar da jinanan raunana Talakawa da ake yi babu kakkautawa a Kasar, bai dace su game baki wuriguda ba su ce sai an canza Jagororin Tsaron Kasar ba?. Eh mana, su je su gana da Shugaban Kasa, kuma gashi akalar “Yan Majalisun Tarayya na Kasa duka na hannunsu ne.

Ba wannan Marubucin kadai ba, da daman jama’ar wannan Kasa na Allah-wadai, tare da kalubalantar wannan mugun salo da Gwamnonin suka yi shuhura a kai, na yin layya da kudaden na kananan hukumomi.

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sen. Shehu Sani, na daga masu fada da yin na-jejjeni-gidan-gwauron da Gwamnoni ke yi da kudaden na kananan hukumomi. A kalaman Sanatan, ya nuna cewa, maimakon Gwamnoni su rika biyan Albashi da gabatar da Manyan Ayyuka da irin wadancan kudade, kawai sai a rika karkatar da su zuwa ga lalitar kashin-kai!

Siyasar Kashin Dankali : Kudaden Kananan Hukumomi

Lusaranci A Majalisun Jihohi Da Na Tarayya

Zamantowar “Yan Majalisun Jihohi da na Tarayya lusarai, ta fuskacin gaza kwatowa Majalisun Kananan Hukumomi hakkokinsu da Gwamnoni ke alkafira a kai dare da rana, sai yanayin ya taimaka zuwa ga mummunan kassara fikokin Kananan Hukumomi ga duk wani batu da ya shafi kudi.

Wancan hali na ko-in-kula da wadancan “Yan Majalisun ke nunawa game da kwato hakkin kudaden Kananan Hukumomin, sai ya jaza musu zama tamkar wasu MABARATA, duk da makudan biliyoyin nairorin da ake antayo musu duk Wata daga Asusun Kudi na Kasa. Duk wani aiki da ya shafi kashe “yan wasu miliyoyin nairori, sai Shugaban Karamar Hukuma ya je ya gwaggwafe a gaban Kwamishinan Kananan Hukumomi gami da yin “yar murya, sannan za a sahale masa gabatar da aikin. Daga nan sai a tsakuro wani abu cikin kudin Karamar Hukumar tasa a zi-zara masa.

A hannun Shugaban Karamar Hukuma ne jama’ar karamar hukuma suka sanya amanarsu ba a hannun Kwamishinan Kananan Hukumomin da Gwamna ya nada ba. Da yawan wasu kwamishinonin kananan hukumomin, ba cancanta ce ke kai su bisa kujerun ba, face alfarmar gwamna. Na’am! Nada Kwamishinan kananan hukumomi ba laifi ne ba, bilhasali ma Doka ce ta sahalewa gwamna yin nadin, amma me zai hana a bai wa kowa ikon da Doka ta ba shi daidai-wa-daida ba tare da yin wani tsinbure ba?

Wancan karfa-karfa da gwamnonin ke yi da kudaden kananan hukumomin, sai yanayin ya jaza mayar da kananan hukumomin da tamkar makabartu, ta fuskar rashin samun ayyukan cigaba a yankunansu yad da ya kamata.

Ga Mutumin Kano, da ma wasu jihohi na wannan Kasa, da za a tambaye shi, shin, wane lokaci ne cikin karamar hukumarsu, aka fi samun kwararar ayyukan cigaba, tsakanin lokacin da Kananan Hukumomi ke karbar kudadensu, da kuma lokacin da gwamnoni sukai tsayuwar-gwamin-jaki a kan kudaden?.

Sanannen abu ne cewa, lokacin da kudaden Ciyamomin ke mirginowa kai-tsaye zuwa ga Lalitarsu, Kananan Hukumomi sun yi abin-kai. An malala tarin ayyuka cikin kananan hukumomin! An debi dubban Matasa aiki. An sami manya, matsakaita da kananan kwangiloli. Sannan, ciniki ya bude a mabanbantan Kasuwanni. Da yawan Matasa masu sana’o’in hannu, suma an dama da su, sun sami amfani a kananan hukumomin, lokacin da hakkin nasu ke riskar su ba tare da yi masa waigi ba.

Kungiyoyin Ma’aikata Sun Fara Magantuwa

Lokuta da dama a baya, Kungiyoyi musamman na ma’aikata, irin su Kungiyar NULGE da NLC, sun sha kokawa game da yanayi na taho-mu-gama da ake samu, tsakanin kudaden kananan hukumomi da asusun hadaka na gwamnatocin jihohin wannan Kasa.

A wasu sashin kalaman Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa, Mr Ayuba Wabba, ya tabbatar da cewa, da za a sakarwa Kananan Hukumomin kudaden nasu kai-tsaye su yi aiki da shi, to fa da maganar rashin tsaro a Nijeriya ya zama tarihi.

Shi kuwa Khaleel, a matsayinsa na Shugaban NULGE, ya sha jagorantar “yan kungiya zuwa ga neman hakkunan Kananan Hukumomin. A kullum, Khaleel na fadin, ba komai suka sa a gaba ba, face gwagwarmayar ganin daukacin kananan hukumomin sun sami cikakken “yancin tafiyar da lamuransu da kansu, ba tare da an yi musu wani katsalandan ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: