Connect with us

Nahiyar Afirka

Taimakon Dala Miliyan 273 Ga Mozambik Sun Gaza, In Ji Sakataren MDD

Published

on

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewar adadin kudaden agajin da kasashen duniya suka tattarawa Mozambik sakamakon bala’in ruwa da iska da ya afka mata sun gaza abin da kasar ke da bukata.

Kungiyoyin agaji na duniya sun yi alkawarin baiwa Mozambik tallafin Dala sama da biliyan guda ne domin shawo kan bala’in ruwa da iskar da suka afkawa kasar har sau biyu cikin mako guda, amma Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewar abin da kasar ke bukata ya zarce Dala biliyan 3 domin dawo da kasar cikin hayyacin ta.

Tun farko dai an tara Dala miliyan 273 wajen gidauniyar gaggawan da aka tarawa kasar. Sakatare Janar Antonio Guterres dake ziyarar gani da ido a kasar, ya ce agajin kudaden da aka tara na gaagwa da kuma sake gina kasar sun gaza abin da ake bukata.

Guterres ya jaddada cewar, wannan bala’i da ya samu Mozambik nada nasaba da sauyin yanayi, kuma Mozambik bata daukar wani mataki ko kadan wajen haifar da matsalar, amma kuma ga shi ana fuskantar radadinsa. Sakataren wanda ya gana da shugaban kasa Filipe Nyusi ya ce ya zama wajibi ga kasashen duniya su kaiwa kasar dauki.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: