Connect with us

Nahiyar Afirka

Tarayyar Kasashen Afrika Ta Nuna Damuwa Kan Katsalandan Din Kasashen Turai A Libya

Published

on

Kungiyar kasashen Afirka wato AU ta bayyana damuwar ta kan yadda ake samun katsalandan daga kasashen waje a Libya, inda ta bukaci kafa wani kwamitin na musamman tsakanin Jakadun Majalisar Dinkin Duniya da na ta domin yin aikin samo hanyar magance rikicin kasar.

Kungiyar ta ce kwamitin zai yi aiki wajen aiwatar da shirin zaman lafiyar Libya kamar yadda masu shiga tsakanin suka shata tare da shugabannin kungiyoyin dake rikici a kasar.

Rahotanni sun ce an samu zazzafar muhawara wajen taron kungiyar, ko da dai shugabanta Abdel Fatah Sisi kuma na hannun daman Khalifa Haftar ya kauracewa zaman taron.

Libya dai ta koma cikin yakin basasa ne tun bayan da Khalifa Haftar mai rike da galibin yankunan kasar ya kaddamar da farmakin kwace birnin Tripoli cikin watan Afrilu.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana cewa fiye da mutane dubu guda sun rasa rayukansu a sabon rikicin na Libya yayin da wasu fiye da dubu 75 suka tsere daga kasar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: