Connect with us

TASKIRA

Turkashi! Wata Garabasar Sai Allah Mahalicci

Published

on

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi ta’ala wa Barakatuhu ‘yan uwa da abokan arziki masu girma masu albarka.

Allah Subhanahu Wata’ala yana cewa a cikin Al-kur’ani mai girma, Sura ta 59 wato Suratul Zumar, Aya ta 53 kaman haka:

Ka ce, Wato Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam kenan: (Allah Ya ce): “Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.”

Wallahi Tallahi, da a ce za mu yi riko da Al-kur’ani da Sunnah, da dukkannin matsalolin da muke fuskantan a matsayin mu na daidaikun mutane ko a matsayin al’umma sun zama tarihi. Ni ban ga abun da ya kai musulunci sauki, dadi da adalci ba wallahi. Shi fa ALLAH be ce sai ka haddace Al-kur’ani ko sai kai malami ne ko malama kafin ka kai matsayin mumini ba, A’a, shi ALLAH abun da kawai yake bukata daga gareka a matsayin ka na bawansa shi ne ka bi umarnin sa da koyarwar fiyayyen halitta. Kar ka manta ba’a nan fa ya tsaya ba, saboda shi ya halicce mu da ni da ku, kuma ya san muna da rauni zamu kauce hanya, za mu yi mishi laifi, za mu tara zunibu, zamu zalinci kawunan mu, sai ya kara da cewa, idan har ka gane ka yi kuskure kuma ka yi nadama, ka tuba, ka koma gareshi, ka roke shi gafara, ya ce ya yi alkawari zai yafe maka. ALLAHU AKBAR!!! Ba shikenan ba fa! Sai ya kara jaddadawa da cewa, duk girman laifin da ka yi fa, In dai ka tuba fisabilillah zuwa gare shi ya ce zai karbe ka hannu bibbiyu saboda shine mai mai yawan GAFARA, MAI JINKAI, kaji fa! Dan ma wai ya kara mana karfin gwiwa, sai ya kara da cewa, zaifa karbi tuban mu akoda yaushe kuma ako wani yanayi sai dai a lokaci guda ne bazai karba ba, shi ne tuban da aka yi kokarin yinta yayin da mutun ya hango mutuwa. Ke/kai kuwa ‘yan uwa shin wai mai muke Jira ne? Kai ka taba ji ko ganin wata #RAHAMA, #TAUSAYI, da #JINKAI kwatankwacin wannan? Wallahi ko da kananan abubuwa muka fara canjawa za mu ga cigaba a rayuwar mu da al’umma gaba daya. Kananan su ne suke haifar da manya.

Misali:

• Duk abun da za ka yi ka fara da Bismillah.

• Duk abun da za ka yi ka fara da dama.

• Yawaita Sallama a tsakaninmu, wanda Manzo Sallallahu Alaihi Wasallam ya fada mana ya kawo soyayya.

• Maimakon zaman gulma da shisshigi mu dinga tunatar da juna Allah.

• Sanar da wani ko wata dan abunda Allah ya sanar da kai komin kankanta shi.

• Yima dan uwanka adduan alheri ba tare da saninsa ba domin kaima mala’iku za su yi maka.

• Duk sadda za ka yi magana ka fadi alheri ko ka yi shiru.

• Ka fita harkar duk abin da babu ruwanka da shi, ma’ana ka bar abun da bai shafe ka ba.

Suna nan da yawa ba za su lissafu ba.

Allah ubangiji ka bude mana zuciya, da idon mu, da Kunne domin mu gane abun da ka aiko mana kuma mu yi aiki da shi, alfarman Manzo Sallallahu Alaihi Wasallam.

Binta Shehu Bamalli

Mrs Mustapha

Muhimman kalmomi a cikin nasihar: #musulunci #ibada #tuba #tunatarwa #alhamdulillah #al’umma #rahama #tausayi #jinkai #coachbabiebamalli #mrsmustaphals.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: