Connect with us

KASASHEN WAJE

UNHCR Ta Nemi Sudan Ta Kudu Ta Magance Matsalar Raba Mutane Da Muhallansu

Published

on

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD(UNHCR) ta yi kira ga jagororin kasar Sudan ta kudu, da su kara zage damtse wajen kawo karshen matsalar raba mutane da muhallansu da ta fi girma a nahiyar Afirka.

Hukumar ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar, yayin murnar cika shekaru 8 da kasar ta samu ‘yancin kanta, inda ta zama jaririyar kasa a duniya cewa, an samu ci gaba, amma har yanzu ba a samu zaman lafiya ba, sannan ba a kai ga warware wasu muhimman batutuwa ba.

Hukumar ta MDD da abokan huldarta, sun kaddamar da gidauniyar dala biliyan 1.4 don samar da tallafin jin kai ga ‘yan gudun hijira. Sai dai kaso 21 cikin 100 na kudaden da ake nema kawai aka tara, yayin da bukatun ‘yan gudun hijirar suka dara kudaden dake hannu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: