Connect with us

Waiwayen Kanun Labarai

Waiwayen Kanun Manyan Labarai

Published

on

Daga Juma’a 2 Zuwa Alhamis 8 Ga Zulqida, 1440 Bayan Hijira

Juma’a 2 ga Zulqida, 1440 (5/7/2019)

Assalamu alaikum barkanmu da juma’atu babbar rana, biyu ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W, dai-dai da biyar ga Yulin 2019. Bitar muhimman kanun labarun namu ta fara da:

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da wani taro da manyan jami’an tsaro na kasar nan a jiya.

2. Wata kungiya mai suna CUPP a takaice ta kai gwamnatin tarayya kara kotu saboda saba wa doka da tsarin mulkin kasar nan, bangaren barin su sakataren gwamnati Boss Mustapha da sauran mukarraban gwamnati su ci gaba da aiki alhali aikinsu ya kare a lokacin da wancan wa’adin na Buhari ya kare, kafin sake zabarsa da rantsar da shi. Wato ya kamata a ce a lokacin da ya rushe ministoci su ma ya rushe su, daga baya da aka rantsar da shi ya kuma nada su idan su din dai yake so ya ci gaba da tafiya da su a wa’adinsa na biyu.

3. Sanata Elisha Abbo da ya ci zarafin wata mata yana hannun ‘yan sanda da ke Abuja kodayake shi ya kai kansa da kansa da suka bukaci hakan.

4. Kotu ta yi fatali da bukatar da kungiyar Miyetti Allah ta kai gabanta, ta a dakatar da dokar nan ta hana kiwon-sake da gwamnatin jihar Binuwai ta kafa a jiharta.

5. Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya sanya hannu a kan dokar hukuncin kisa ga duk kidinafan da aka kama da laifin kidinafin.

6. ‘Yan bindiga sun kai farmaki kauyukan Dan Musa da Kankara da sauransu da ke jihar Katsina, suka kashe mutum a kalla goma sha uku.

7. ‘Yan Nijeriya su tara na cikin mutum hamsin da uku da aka kashe a Libiya a lokacin da aka kai hari wani sansani.

Af! A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a, don karanta rubutuna na wannan dandali na fesbuk, da na yi daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.

Asabar 3 ga Zulqida, 1440 (6/7/2019)

A asabar, uku ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W, dai-dai da shida ga Yulin 2019, kanun labarun su ne:

1. Yau asabar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Nijar don halartar taron kungiyar tarayyar Afirka A.U. a takaice.

2. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Boss Mustapha a matsayin sakataren gwamnatin tarayya, da Abba Kyari a matsayin shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa. Kasa da sa’a ashirin da hudu da barazanar kai gwamnatin tarayya kotu da wata kungiya ta yi a kan batun. Sabon nadin nasu ya fara aiki ne daga ranar ashirin da tara ga watan Mayu na 2019.

3. Kotu ta ba da umarnin a kwace wasu gwalagwalai da sarka da agogo da kudinsu suka kai dala miliyan arba’in na Diezani Allison-Madueke, karbewa ta dan wani lokaci saboda zargin gwalagwalan na cikin abubuwan da ta wawura a lokacin da take ministar mai, kuma a yanzun ta makale a Ingila. Gwalagwalan sun kai guda dubu biyu, da dari da arba’in da tara.

4. ‘Yan sanda sun ba da belin Sanata Elisha Abbo da ake zargin ya ci zarafin wata mata mai shayarwa. Kuma na ga shugabar wata kungiya mai suna NAPTIP a takaice na nuna takaicin yadda matar ta kyale sanatan na kai mata duka ita ba ta rama ba. Ta ba da shawarar ya kamata a koya wa mata TAEKWANDO wato fada irin na Cainis ta yadda duk namijin da ya nemi cin zarafinsu su casa shi.

5. Sojoji da ke rike da mulkin Sudan da kungiyoyin da ke zanga-zanga sun yarda su raba iko tsakaninsu na tsawon shekara uku kafin gudanar da zaben shugaban kasar.

Mu yini lafiya.

Af! Yau dai ban manta ko tuna wani abin daban ba.

Lahadi 4 ga Zulqida, 1440 (7/7/2019)

A lahadi, hudu ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi muhammad S.A.W, dai-dai da bakwai ga Yulin 2019, kuwa:

Idan an lura kwana biyu ban yi magana a kan wutar lantarki ba, kuma kusan kullum sai an samu wanda ya tambayeni wutar ta gyaru ne ba mu ji ka yi tsokaci ko batu a kai ba? To a gaskiya wuta dai babu ita. Na ma lura da yake sun san da karfe hudu na asubah nake rubutu sai su kawo wutar wuraren karfe uku da rabi na asubah don in ce akwai wuta ko ma in yi shiru. Karfe biyar na asubah zuwa karfe shida sun dauke. Ba za su dawo da ita ba, sai can wuraren la’asar. Idan sun kawo ta dade ta kai karfe biyar. Idan suka dauke karfe biyar, sai can wuraren karfe takwas na dare su dawo da ita. Karfe goma na dare zuwa sha daya sai su dauke, sai kuma wuraren karfe uku ko uku da rabi na asubah. Ka ga kuwa har yanzun ba wuta sai karbar kudin wutar da talaka bai sha ba, kuma a zamanin mulkin Baba mai gaskiya

Sai kuma batun karin albashi wato New Minimun Wage da ma’aikata ke ta wasuwasin anya gwamnatin nan ba sai har ta gama wa’adin nata na biyu ba ta yi karin ko taro ba kuwa? Don an ce kwamitin da ke wakiltar gwamnati wajen zaman fitar da jagoran yadda za a yi wa kowanne ma’aikaci karin, na nuna babu kudin da gwamnati za ta iya biyan karin. In har za a kara ma’aikaci bai fi a kara masa irin naira dari tara zuwa naira dubu daya ba. Wasu na zargin kungiyoyin kwadago na tsoro ko shakkar zuwa yajin aiki ne saboda tsoron talaka ba zai ba da goyon baya ba, saboda tsananin son da yake yi wa Baba Buhari.

Sai batun tsaro da shugaban kasa, da Yemi Osinbanjo da Buratai ke kara nanata cewa ba za a taba kyale ana ta kashe mutane ba. Sai dai wasu na cewa tatsuniya ce da suka saba tunda har yau ana ci gaba da kashe jama’a a yankin jihar Katsina zuwa Zamfara, ga tarin ‘yan gudun hijira a sansanoni daban-daban a mulkin Baba Buhari.

Sai batun tsarin samar da RUGA da gwamnatin tarayya ta sanar za ta yi, da su Wole Soyinka suka ce ba su yarda ba, gwamnatin tarayya ta ce ta fasa, lamarin da bai yi wa musamman mutanen Arewa dadi ba. Har wasu ke zargin cewa su ne ‘yan lele, sai yadda suka ga dama ake yi a kasar nan a mulkin Baba Buhari.

Sai batun tafiye-tafiye da wasu ke gunagunin Baba Buhari ya fi mayar da hankali ga yawo kasashen duniya maimakon ya zauna gida ya fuskanci matsalolin da ke addabar talakan da ke masifar sonsa. Suka ce yana da mataimakinsa Yemi da sauran mukarrabansa da zai iya turawa kasashen suna wakiltarsa ba dole sai ya je ba. Har wasu na zargin kurciya suka yi wa Baba Buhari ya kasa zama.

Sai batun sabbin nade-nade musamman na ministoci da wasu ke gulmar Baba Buhari na shirin mayar da yawancin tsofaffin ministocin ko ma dukkansu. Ga jan kafa yana yi wajen nade-naden da wasu ke cewa ya kamata tun ma kafin a rantsar da shi ya gama. Ga su Boss Mustapha da Abba Kyari sai da wata kungiya ta yi wa Baba Buhari barazana, sannan cikin kasa da sa’a ashirin da hudu ya sake nada su.

Jama’a yau sharhi ne takaitattu da yake karshen mako ne babu labaru sosai sai na bikin ranar sojoji da aka fara.

Litini 5 ga Zulqida, 1440 (8/7/2019)

Bitar kanun labarun a litinin, biyar ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W, dai-dai da takwas ga Yulin 2019 sun kunshi:

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta walwalar kasuwanci a nahiyar Afirka a Niamey ta kasar Nijar.

2. Gwamnatin tarayya ta ci gaba da karfafa wa sojojin kasar nan gwiwar yakin da suke yi da ‘yan ta’adda.

3. Sojojin sama na Nijeriya sun lalata wurare daban-daban na mahara da ke Bakassi a jihar Barno da kashe wasu dakarunsu masu yawan gaske.

4. Kamfanonin raba wutar lantarki da aka fi sani da DISCOs su hudu, sun samu riba ko kudin shiga naira biliyan arba’in da shida da rabi da ‘yan kai ga kuma tallafa musu da aka ce kungiyar USAID za ta yi.

5. Kungiyar kula da bunkasar tattalin arziki da kare hakki mai suna SERAP a takaice, ta yi na’am da hukuncin kotu, na a fallasa dukkan kudaden da aka bai wa ‘yan kwangilar wutar lantarki, kama daga gwamnatocin da, zuwa na yanzun, suka cinye kudin, suka tsere ba tare da sun gyara lantarkin ba.

Mu yini lafiya.

Af! Ga matafiya Zariya zuwa Kaduna musamman idan yamma ta karato zuwa almuru har ma in dare ya yi ana tuki cikin gosilon nan, ko direba ko fasinja ko abokin tafiya, to a dinga hattara da yin waya ko amsa waya saboda akwai masu fisge waya suna aukawa daji a guje. Haka nan matafiya da ke isowa gadar Kawo daga almuru zuwa cikin dare, akwai barayin waya ko kwacen kudi ko kaya da masu yi wa mata fyade a kusa da gadar. Majiya karfi ne da makamansu har ana rade-radin wai sun fi karfin sojoji da ‘yan sanda da ke wuraren gadar ta Kawo.

Talata 6 ga Zulqida, 1440 (9/7/2019)

A talata, shida ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W, dai-dai da tara ga Yulin shekarar 2019, kanun labarun su ne:

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iso Abuja bayan taron kungiyar tarayyar Afirka da ya halarta a Niamey ta kasar Nijar.

2.Mele Kyari, sabon shugaban rukunin kamfanin mai na kasa NNPC ya kama aiki. Dafta Maikanti Baru ya yi ritaya.

3. Wata kotun majistare da ke Abuja ta ba da belin Sanata Elisha Abbo da ake zargin ya ci zarafin wata mai shayarwa. An ba da belinsa a naira miliyan biyar. Sai dai a yanzun ya fara musanta ya aikata laifin, alhali har taro ya kira na manema labaru yana neman gafarar abin da ya aikata kuma ga faifan bidiyo na yana kai wa matar duka da kamara ta nada.

4. Sojoji sun ceto wasu manoma goma sha uku, suka murkushe wani dan bindiga a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

5. ‘Yan sanda sun ceto mutum goma sha daya a Zamfara.

6. Mutane goma sha tara suka rasu, bakwai suka ji rauni a wani hadarin mota da ya auku a Kano.

7. Atiku da PDP sun soma gabatar da tarin shaidu da suke da su a karar da suka shigar a kan zaben shugaban kasa Buhari.

Af! Gwamnatin jihar Kano ta sa an rushe gidan da aka ajiye Magajin Garin Daura da ke Kano a lokacin da aka yi garkuwa da shi.

Laraba 7 ga Zulqida, 1440 (10/7/2019)

A laraba, bakwai ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W, dai-dai da goma ga watan Yulin 2019, kanun sun hada da:

1. Shugaban ‘Yan sandan Nijeriya ya ba ‘yan sanda umarnin sanya ido a ciki da wajen Abuja sa’a ashirin da hudu babu kakkautawa.

2.Majalisar Dattawa na wani yunkuri na tabbatar da kwakkwaran hukunci ga masu yi wa musamman yara mata kananan fyade.

3. Kwamitin Majalisar Dattawa ya gurfanar da Sanata Elisha da ake zargi da cin zarafin wata mai shayarwa a gabansa, bayan an yo belinsa daga kotu.

4. Hukumar zabe ta kasa ta ce a cikin shawara guda sittin da tara da turawan da suka zo sa ido a zabukan da suka gabata suka bayar don zabuka su inganta a kasar nan, guda ashirin da bakwai kawai za ta dauka.

5. ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a jihar Katsina.

6. Wata kungiya ta ce ba ta amince da yunkurin yin RUGA a al’umar Bokko da ke jihar Filato ba.

Alhamis 8 ga Zulqida, 1440 (11/7/2019

A alhamis, takwas ga watan Zulkida, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W, dai-dai da goma sha daya ga Yulin 2019, kanun labarun su ne:

1. A makon nan ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisar Dattawa sunayen wadanda yake so su amince masa ya nada su ministoci.

2. Hukumar kula da al’amuran masu shari’a/alkalai ta kasa NJC a takaice ta mika amincewarta ga shugaban kasa ya tabbatarwa Muhammad Tanko kujerar Onnoghen da yake riko ta babban mai shari’a na kasa CJN a takaice.

3. Kidinafas na ci gaba da sace masu zuwa gonakin da ke tsakanin Kaduna da Abuja.

4. A jihar Taraba ‘yan bindiga sun kashe mutum a kalla hudu.

5. A jihar Nasarawa jami’an tsaro sun kama wadanda suke zargi da aikata laifuka daban-daban har da kidinafin su hamsin da takwas.

6. Talakawan Nijeriya na ci gaba da yin Allah Ya isa saboda biyan kudin wutar da ba su sha ba.

7. Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta zauna da ‘yan Shi’a.

Mu yini lafiya.

Af! Na ga Sanata Elisha Abbo yana ta da jijiyoyin wuya ga wakilan kwamitin majalisar, da majalisar ta kafa don tambayarsa zargin da ake masa na ya yi wa wata mai shayarwa duka. Na ga yana yi wa musamman matar da ke cikin kwamitin fada cewa shi ma sanata ne kamar su. Wannan ya sa na fara wani tunani. Anya..? Hmm! Ba kwa ji mutuwar sarki a bakina ba. Na yi nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: