Connect with us

LABARAI

Yadda Maganganu A Soshiyal Midiya Suka Dagula Lissafin Ja’afar Aliyu A Majalisar Dokokin Kaduna

Published

on

Majalisar dokokin Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Kakakin Majalisar, Honarabul Aminu Shagali, ta ki amincewa da tantance sunan Aliyu Jafar, daga karamar hukumar Kauru a matsayin Kwamishinan gona na jihar Kaduna, kamar yadda tun da farko Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed Elrufai, ya turo masu sunansa domin su amince su tantance shi matsayin kwamishin gona na jihar Kaduna.

Aliyu Jafar, wanda ‘Da yake ga Sarkin Kauru, Alhaji Jafaru Abubakar, ya sami tangarda ne a yayin zaman majalisar da ya gudana domin tantance shi.

A yayin zaman tantancewar dai, kakakin majalisar Honarabul Aminu Shagali, ya bayyana cewa, “ Malam Aliyu Jafar, mun duba duk takardunka mun gamsu da karatunka da kuma kwarewarka, sai dai muna so ka yi mana karin bayani dangane da Kalaman batancin da ka taba yi  a shafinka na fesbuk dangane da wannan gwamnati na Jam’iyyar APC karkashin jagorancin Malam Nasiru Elrufai.”

Duk kokarin da ‘yan majalisar dokokin Jihar Kaduna suka yi na ganin Aliyu Jafar ya kare kansa dangane da wannan tuhuma da suke masa, amma abin ya ci tura, domin ya kasa cewa uffan a kan wannan lamari. Dangane da haka ne, ‘yan majalisar dokokin jihar Kadunan karkashin jagorkncin Kakakin majalisar, suka yi fatali da sunansa a matsayin Kwamishinan gona na Jihar Kaduna.

Ga abin da Aliyu Jafar, ya rubuta a shafinsa na fesbuk kamar yadda wakilinmu ya ruwaito;

“Gwamnatin Malam Nasir yaudarar mutane kawai take yi.  Babu wani abin da ta zo da shi na sauya Jihar Kaduna. Don haka, ka da mutane su tsammaci wani abu daga wajen gwamnati. A jira wadanda da gaske suke ba yaudara suka zo da sunan sauya jihar ba.”

A wani bangaren kuma, ya rubuta cewa,”  A daina hadani da Malam Nasir wanda yake ganin ya fi iyawa kansa iyawa, saboda shi Malam yana daukan kansa ya fi kowa kuma ya san komai. Ni  mutum ne mai daraja da daukaka domin haka cin mutunci ne a hadani da Mai Girma Gwamna a ta kowane fanni.”

Wannan sune wasu daga cikin kalaman batanci da majalisar dokokin Jihar Kaduna ke tuhumar Aliyu Jafar da su. Duk irin kokarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin Aliyu Jafar, abin ya ci tura, domin duk wayoyinsa a kashe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: