Connect with us

Uncategorized

‘Yan Nijeriya 163 Sun Sake Dawowa Daga Libya

Published

on

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya wato NEMA ta karbi ‘yan Nijeriya 163 da aka bari a yashe a kasar Libya, inda bayan agaji da suka samu, aka dawo da su daga kasar ta Libya zuwa gida Nijeriya.

Alhaji Idris Muhammed, Kodinetan hukumar NEMA din a garin Legas shi ne ya tabbatarwa da manema labarai hakan a ranar Juma’a a garin Legas.

Muhammed ya ce sun isa filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas da misalin karfe 8.33 na daren ranar Alhamis daga wani jirgin sama na  Al Buraq Air aircraft mai lamba 5A-DMG.

Ya ce; wadanda suka dawo din sun samu agajin hukumomin Nijeriya da kungiyoyin kasashen waje da suka hada da IOM da kuma EU a karkashin shirin taimakon da ake bayarwa na dawo da su kasashensu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: