Connect with us

LABARAI

‘Yan Sara-suka 500 Sun Tuba A Bauchi

Published

on

A jiya Alhamis ne wasu matasa ‘yan daba da aka fi saninsu da ‘yan Sara-suka, suka tuba hadi da mika makamansu ga ‘yan sanda a Bauchi.

‘Yan sara-sukan sun ce sun ajiye makaman fadarsu ne a bisa nazarin da suka yi da kuma son zama cikin al’umma lami-lafiya.

Sai dai, matasan sun koka sosai da aiyukan ‘yan kwamitin sa-kai, ‘yan kato da gora a bisa zargin da matasan suka yi na cewar suna wuce gona da iri a kansu, don haka ne suka ce, bayan tubarsu suna neman gwamnati ta soke su domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’ar jihar da wajenta.

A zantawarsa da wakilinmu, daya daga cikin wadanda suka tuba mai suna Abdurrazak Muhammad da ke unguwar Bakaro wanda aka fi sani da Mataro, ya ce sun tuba, abin da ya rage shi ne a samar musu da aiyukan yi don gudun komawarsu gidan jiya.

“Shi wannan harkar da ake magana a kai na batun jagaliyanci da dabanci Sara-suka da sauransu mun fada ciki ne a sakamakon rashin abun yi. Na yi makaranta har zuwa sakandari amma na gagara karawa gaba, na kuma gagara samun aiki, tun shekaru sama da biyar da suka gabata na fada wannan harkar. Amma ina godiya wa Allah da ya sa yau na tuba na ajiye makamina,”

Ya fadi bukatarsu a takaice, “Eh mun tuba, abu na farko gwamnati ta soke ‘yan kwamiti (kato da gora) ta haramta su kwata-kwata, sannan ta samar mana da aiyukan yi. Dalilinmu da ya sa muka ce a cire kwamiti suna zalumci a maimakon su yaki zalumci, tun da kowace unguwa akwai mai unguwa duk yaron da ya aikata ba daidai ba a kai kararsa wajen mai anguwa a hukunta shi. Amma zancen ‘yan kwamiti sam a ciresu muddin zaman lafiyar ake so,” A cewar shi.

Akalla mutane nawa ka sara a rayuwarkata da dabanci? Sai ya amsa da cewa, “oga gaskiya fa mun tuba, wannan zancen naka dogon tone-tone kake son a yi, an sari da dama, an ji min ciwo, ni ma na ji ma wani, an ji ma wani nawa, na ji ma wanin wani, amma ai an tuba aka ce ko?,” A fadin shi.

Shi ma Abba Adamu wanda aka fi saninsa da (Kunnuwa) daga unguwar Bakin Kura, ya ce jami’an ‘yan sanda su yi kokarin daidaita tsakanin matasan da suke zaman doya da manja a unguwanninsu domin daurewar zaman lafiya. Ya shaida cewar yanzu haka wasu ba su iya watayawa a cikin jihar duk da sun rigaya sun tuba, don haka ne ya nemi jami’an ‘yan sanda su agaza musu wajen shawo kan wannan matsalar domin komai ya tafi daidai.

“Mun ajiye burmunamu da su barandaminmu a nan ne yau don mun daina Sara-suka. Muna fatan kowa ya yafe mana, muna son gwamnati ta shiga tsakaninmu da ‘yan kwamiti domin suna zalumtarmu; gwamnati ta ba mu sana’ar yi ko mu ci gaba,” A cewar Kunnuwa.

Shi ma wani matashi mai suna Minka’ilu da ke unguwar Kofar Dumi daga cikin wadanda suka ajiye makamansu hadi da yin saranda, ya ce “Mun zo ne don mu sallama mu hakura da wannan dabancin, mun yi hakan ne domin muna fatan wannan gwamnatin za ta jawo mu a jika ta samar mana da aiyukan yi. Muna son kuma abokanmu da suke wasu unguwanni da ake rashin jituwa muna son a sasanta, don haka an yi haka, yau har musabaha muka yi da wadanda a da baya muna fada tare,” A fadin shi.

Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, Habu Sani Ahmadu, ya shaida cewar wannan babban ci gaba ne ga yaki da matsalar tsaro da suke kokarin yi a fadin jihar, yan mai cewar tun zuwansa jihar, ya himmatu wajen yaki da matsalar Sara-suka, garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran matsalolin tsaro da suke addabar jihar.

Ya jawo hankalin matasan da suka tuban da cewar su daure su fuskacin turbar da ta dace, a fadinsa jami’an ‘yan sanda za su bi dukkanin matakan da suka dace wajen taimaka musu domin ganin rayuwarsu ta inganta.

CP Sani ya shaida cewar kofarsu a bude take su amshi karin wasu matasan muddin suka yarje za su tuba, ya ce koda basu tuba ba, to za su tabbatar da tursasa musu daina Sara-suka domin ba za su lamuncera ba.

Da yake jawabinsa a wajen amsar tubabbun ‘yan Sara-sukan sama da 500, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya nuna gayar farin cikinsa a bisa wannan babban ci gaban da aka samu, yana mai fatan Allah ya sanya jihar ta amfana da matasan da suka tuba.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Abubakar Kari, ya kuma shelanta musu cewar gwamnatinsa yanzu haka tana shirye-shiryen lalubo bakin zaren yadda za ta samar wa matasa da aiyukan yi domin su zama masu dogaro da kansu wanda jihar za ta ci gajiyarsu dari bisa dari.

Ya hore su da cewar kada su koma gidan jiya na yin aiyukan da basu dace ba; kana ya tabbatar musu da cewar gwamnati tana kan tsara musu tsari masu nagarta wanda kwanan nan za su fara cin gajiyarsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: