Connect with us

WASANNI

Arsenal Tana Dab Da Kammala Daukar Malcom Daga Barcelona

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tana dab da kammala cinikin dan wasan gaba na kungiyar Barcelona, Malcom, bayan da tun farko Eberton ce take zawarcin dan wasan dan kasar Brazil.

Tun farko dai Eberton ce ta taya dan wasan fam miliyan 31 wanda kuma tuni suka fara tattaunawa da Barcelona akan matashin dan wasan mai shekara 22 a duniya sai dai Arsenal ta shiga cinikin kuma tuni hankalin Malcom din ya karkata ga Arsenal.

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Enestor Balberde ne dai ya tabbatarwa da Malcom cewa baya cikin tsarinsa na wannan shekarar hakan yasa dan wasan ya fara tunanin kungiyar da zai koma domin cigaba da buga wasa.

Barcelona dai ta kashe kudi fam miliyan 36 wajen sayan dan wasan daga kungiyar kwallon kafa ta Bourdeaud dake kasar Faransa sai dai a kakar wasansa ta farko wasanni shida kacal aka fara bugawa dashi a laliga.

Tuni dai Arsenal tafara jan hankalin dan wasan daya fasa komawa Eberton din domin ya koma birnin Landan da buga wasa sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa Arsenal suna son daukar aron dan wasan ne na tsawon kakar wasa daya kafin kuma su biya kudinsa a kakar wasa ta gaba.

Dan wasan gaba na kungiya kwallon kafa ta Crystal Palace, Wilfred Zaha, shine wanda Arsenal ta nema tun farko kuma ta taya dan wasan fam miliyan 40 yayinda Palace din tace sai Arsenal ta biya fam miliyan 80 akan dan wasan mai shekara 26 a duniya.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: