Connect with us

LABARAI

Buhari Ya Yi Ta’aziyyar Diyar Shugaban Kungiyar Yarabawa Ta Afenifere Da Aka Kashe ‘Yarsa

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ta’aziyyar diyar shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere Pa Reuben Fasoranti. Wacce aka kashe din sunanta Funke Olakunrin. Rahotanni sun nuna cewa; a ranar Juma’a aka kashe ‘yar ta sa a titin Kajola zuwa ore a jihar Ondo. ‘Yan Sanda sun bayyana cewa; ‘yan fashi ne suka kashe ta.

Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a ya ce; shugaban kasar ya yi addu’ar Allah ya jikan mamaciyar tare da bai wa makusantanta hakurin jure rashin da suka yi.

Sannan ya ba da umurnin a gudanar da kwakkwaran bincike domin bankado wadanda suke da hannu wajen kashe ta don zartar musu da hukunci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!