Connect with us

WASANNI

Dangote Da Otedola Sun yi Wa ‘Yan Wasan Super Eagles Alkawarin Kudade

Published

on

Manyan Attajiran Nijeriya guda biyu, Aliko Dangote da Femi Otedola sun yiwa ‘yan wasan tawagar Super Eagles ta Nijeriya dake gasar cin kofin Afirka a Masar alkawarin kudade idan sun samu nasara a sauran wasannin su guda biyu da suka rage, bayan nasarar da suka samu a wasan daf da na kusa da na karshe kan Afirka ta kudu.

Yayin ziyarar da suka kaiwa kungiyar a otel din da suke a Birnin Alkahahira, Aliko Dangote yayi alkawarin biyan Dala dubu 50,000 kan kowacce kwallo guda da kungiyar ta jefa a wasannin da za suyi nan gaba, yayin da Femi Otedola yayi alkawarin Dala dubu 25,000 kan kowaccee kwallo guda daya.

Kafin wannan alkawarin, wani attajirin Nijeriya mai harkar mai, Captain Hosea Wells Okunbo ya yiwa kowanne dan wasa guda daya alkawarin Dala dubu 20,000 idan sun doke kamaru kuma ya biya su bayan nasara da suka samu, kana shima Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya baiwa kowanne dan wasa Dala dubu 5,000 saboda gagarumar nasara da suka samu akan Kamaru.

Ita ma kamfanin man AITEO dake hadin gwuiwa da Hukumar kwallon kafar Najeriya ta biya Dala dubu 25,000 akan kowanne kwallo guda da Najeriya ta jefa a wasan Kamaru wanda kuma suma an biya.

Sai dai dan wasa Ahmad Musa ya bayyana cewa wannan alkawarin da attajiran Najeriya suke musu bashi ne yake sawa suke kokari ba inda yace daman tawagar tana zuciyarsu kuma zasu iya buga wasa ba tare da an basu kudaden garabasa ba.

Najeriya dai zata fafata wasan kusa dana karshe da tawagar ‘yan was am kasar Algeriya a gobe Lahadi da misalign karfe takwas kuma idan Super Eagles din ta samu nasara zata fafara da wadda tayi nasara  tsakanin kasar Senegal da Tunisia.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: