Connect with us

TATTAUNAWA

Jaddada Mahimmancin Makarantun Tsangaya Ne Mafita Ba Hana Bara Ba – A’ishatu Lurwan

Published

on

HAJIYA A’ISHATU LURWANU ta na daya daga cikin wakilan kwamitin amintattu na kungiyar tattalafawa Almajiri da ake kira a Turance “Almajiri Support Imitatibe”  ko kuma da aka fi sani da kungiyar Lillahi da ke a jihar Kaduna.

Kungiyar tana  karkashin Makaranta mai zaman kanta da ake kira Al-ansar Academy da ke kan titin Gwamna cikin  jihar Kaduna.

A hirarta da ABUBAKAR ABBA ta bayyana dalilin kafa kungiyar, yunkurin Gwamnatin Tarayya na dakatar da bara da kuma nasarorin da Al-ansar Academy ta samu tun bayan kafata.

Me ya ba ku kwarin gwiwar kafa wannan kungiya ?

Gaskiyar Magana, tun kafin mijina ya bar aiKin soja, wannan abin yana damu sa soasi, kullum yana maganar ya za a yi a shawo kan matsalar barace-barace domin abin a Arewacin Nijeriya ya fi shafa. Kuma yana yawan yin rubuce-rubuce a karkashin “Lillahi Charity” duk abin da zai rubuta a karkashin kungiyar shi ne abin da zai al’umma ta farka, saboda haka ya yi rubuce-rubuce a kan bara, muna da abubuwa da yawa da muke yi a karkashin Lillahi, amma bara ita ce ta daya.

Allah ya ba mu damar yadda za mu tafiyar da kungiyar, inda kafin ka ce kwabo, ta samu karbuwa a gun mutane domin su ma abin ya dame su kowa sai ka ga yana son ya shigo a yi tafiyar da shi don ya bayar da ta sa gudummowar.

A yanzu kun kai ku nawa a kungiyar?

Gaskiya mun kai dari biyu da wani abu, wasu kuma za su ce abubuwa ya yi masu yawa, amma duk lokacin da ake nemam wani taimako mu kira su don su bada nasu ko kudi ko wani aiki da za mu yi.

Ya ya keke ganin yunkurin Gwamnatin Tarayya na dakatar da Almajiranci ?

Hakan zai taimaka wajen yi wa tsarin garambawul kuma barar nan za ka ji Malam tsangaya suna cewa ba Almajiransu kadai ba ne suke yin bara ba suna amfani da wannan damar ce suna fita suna yin bara a saboda hakan, su ma suka samu damar fitowa suna yin barar, wasu  za ka ga daga gidajen su suke fitowa zuwa yin barar ba lallai daga makarantarsu suke fito wa ba, amma su Almajiran daga makarantun suke fitowa zuwa barar abincin, su kuma koma makarantunsu. Wasu na nan suna yin bara har da tsofaffi, matan aure da kuma ‘ya’yansu wasu mabarantan kamar guragu har haya suke yi na wadanda za su tura su a keken guragu zuwa bara, to, ka ga wannan barar ba lallai sai Almajirai ba, mutane da yawa ma suna fitowa yin bara.

Ina ganin idan Gwamnatin Tarayya za ta fito da makarantun tsangayar Almajirai, wato a fito masu da yanayin da zai kyautata karatunsu, wajen kwanciyarsu, samar masu da abinci, kiwon lafiyar su kamar yadda akeyi a lokacin Turawa suka kawo mana ilimin Boko ai ka ga a wancan lokacin tsangayar Almajirai ce aka sani amma yanzu abin ba haka ba ne.

Ya kamata ‘yan Majalisun na kasa da na jiha da kuma mu masu ruwa da tsaki a kafa wata doka ta musamman da za ta hana barace-barace sannan kuma a kafa makarantun tsangaya inda Almajiran za su dinga yin karatunsu. A da gwamnati da iyaye suna ciki amma yanzu kamar ba sa yi.

Sannan kuma masu kudi a wancan lokacin, suna kawo zakka da ake kai wa tsangayu, a da za ka ga idan yaro ya fita a wani gida za ka ga yake yin aiki, inda za ka ga har ya zama dan gidan.

Kamar yadda Shugaban kasa ya ce yana son ya yi tsari. Ka ga a lokacin Jonathan ya kirkiro da makarantun tsangaya, amma har yanzu abin ba a yi komai ba, yakamata Shugaba Buhari ya jadda tsarin tsangaya ba wai a yi watsi da su ba.

Sanan kuma Shugaba Buhari ya kawo wani kundi na tsarin da zai jaddada  mahimmancin yin amfani da makarantun tsangaya kuma Shugaba Buhari, ya fito da wni tsari da zai tabbatar da kowanne yaro yana makaranta in aka kama yaro a san matakin da za a dauka.

Yaushe kuka kafa makarantar ?

Ba ta wuce shekara uku da kafa ta ba.

Me ya sa kuka kafa makarantar ku ta Al-ansar  Academy ?

Mun kafata ne don bayar da tamu gudnummowar wajen cike gibin ilimin Boko da ake da shi a Arewacin Nijeriya sannan mun duba a Kaduna, in ka duba, guda nawa ne irin wadannan makarantun na Musulmai toh wannan babban kalubale ne a gare mu.

Sannan kuma kishi ne ya sanya muka kafa sai muka ga ya kamata mu yi a Musulunce yadda yara za su tashi da tarbiyyarr Musulunci.

Ko za ki  ga ya mana wasu daga cikin nasarorin da kuka samu ?

A yanzu munada dalibai kusan dari uku da wani abu mun kuma fara ne da dalibai ashirin da wani abu muba kuma tabbatar da yaran daliban suna samun ilimin Boko dana addinin Musulunci.

Mun halarci gasa dadan-daban, inda muka samu nasarori da dama.

Wanne kira za ki yi ga iyaye, musamman mata wajen kula da tarbiyar yayansu ?

Wasu iyayen suna da sakaci sosai, sai kaga wasu iyayen wannan zamani su kansu ba su da tarbiyya don Allah iyayen wannan zamani ku inganta tarbiyar yayanku domin shi kanshi ilimin Muhammadiyya da na Bokon idan ba tarbiyya ba zai amfani yaro ba.

Iyaye musamman mata su kasance suna bibiyar ‘ya’yansu don rashin tarbiyya yana tabarbarar da abubuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: