Connect with us

WASANNI

Ko Ka San Dalilan Da Suka Sa Nijeriya Ta Doke Afrika Ta Kudu?

Published

on

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta kai wasan kusa da na karshe a gasar Cin Kofin nahiyar Afirka da ake yi a kasar Masar, bayan da ta doke Afirka ta Kudu 2-1 a ranar Laraba kuma Najeriya ta kai wannan matakin duk da ka sa halartar wasannin shekarar 2015 da aka yi a Ekuatorial Guinea da wanda aka yi a Gabon a 2017.

Super Eagles ta samu karfin gwiwar zuwa karawar kusa dana kusa dana karshe, bayan da ta fitar da mai rikke da kofin wato Kamaru, ita kuwa Afirka ta Kudu mai masaukin baki kasar Masar ta fitar a wasannin.

Kwararrun ‘Yan Wasa

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta je kasar Masar da kwararrun ‘yan wasa 22 da ke buga wasa a wajen kasar, in ban da mai tsaron ragar Katsina United, Ikechukwu Ezenwa ita kuwa Afirka ta Kudu ta je ne da guda shida da ke buga wasa a wajen kasar, kuma ba a fitattun kungiyoyin Turai da ake ji da su a fagen kwallon kafa  ba.

Karawar da kungiyoyin biyu suka yi ranar Laraba, Najeriya ta fara da kwararrun ‘yan wasanta 11, kuma canji ‘yan wasa biyun da ta yi suma kwararru ne suka shiga saboda sauyin da Najeriya ta yi shi ne wanda Moses Simon ya canji Ahmed Musa, sai Balogun da ya maye gurbin Aled Iwobi.

Afirka ta Kudu ta fara wasan da kwararrun ‘yan wasanta hudu daga 11 da suka fara wasa da ya hada da Bongani Zungu da ke wasa a Faransa a kungiyar Amiens da Lebo Mothiba da ke wasa a Faransa a kungiyar Strasbourg.

Sai Kamohelo Mokotjo da ke wasa a Ingila a kungiyar Brentford da kuma Percy Tau da ke wasa a Belgium a kungiyar Union Saint-Gilloise sai kuma dan wasa kwararre da Afirka ta Kudu ta saka a wasan shi ne Lars Beldwijk da ke wasa a Netherlands a kungiyar Sparta Rotterdam wanda ya maye gurbin Lebo Mothiba.

Hakika kwarewa da gogewa ta taka rawar ganin da ya bai wa Najeriya damar kai wa zagayen gab da karshe saboda ‘yan wasa irinsu Wilfred Ndidi da Etebo da ahmad Musa da Ighalo duk sun buga manyan kungiyoyin da duniya ta sani.

Samuel Chukweze

Bayan da Samuel Chukwueze ya buga wasan farko da kasar Burundi, daga nan ne aka ajiye dan kwallon a benci, bai buga wasa uku ba sai a karawar Kuarter finals aka sa shi a wasa inda ya ci kwallo, sannan ya taka rawar gani a fafatawar.

Kwallon da Chukwueze mai buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Billareal ya zura a raga, itace  ta farko da ya ci wa Super Eagles, ya kuma nuna a shirye yake ya zama kashin bayan tawagar nan gaba.

Sai dai tawagar Afirka ta Kudu tana fama da karancin zura kwallaye a raga a wasannin da ake yi a Masar, inda guda biyu kacal ta ci kawo fitar da ita da aka yi a karawar daf da na kusa da na karshe kuma kwallayen da ta zura a raga sun hada da 1-0 da ta ci Namibia a wasanin rukuni da kuma daya mai ban haushi da ta ci mai masaukin baki Masar, a wasan zagaye na biyu, daman ta kai matakin gaba a alfarma.

Kuma Afirka ta Kudu ba ta cin kwallo a minti 45 din farko, saboda haka wannan ya kawo mata tsaiko har Najeriya ta zura mata daya a raga a minti na 27 sannan kuma kafin aje hutun rabin lokaci Afirka ta Kudu ta kasa kai wani gagarumin hari a 45, wanda hakan matsala ce ga tawagar da ke son kai wa karawar daf da karshe, jumulla hari biyu ta kai da suka nufi raga a kacokan  wasan.

A karon farko da aka gabatar da na’urar da ke taimakawa alkalin wasan tamaula yanke hukunci BAR ta taka rawa a karawar tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu kuma Percy Tau ne ya yi bugun tazara saura minti 20 a tashi wasan Thulani Hlatshwayo ya saka wa kwallon kai daga nan Bongani Zungu shi ma ya sa kai ta fada raga, sai dai mataimakin alkalin wasa ya daga tuta cewar an yi satar gida.

An yi duba na tsanake kan abin da ya faru kafin kwallon ta shiga raga, inda da farko kai kace Hlatshwayo ne ya taba kwallon daga bugun tazara, amma da aka yi duba na tsanaki Odion Ighalo ne ya sa mata kai hakan ne ya sa alkalin wasa bai karbi hukuncin mataimakinsa Redouane Jiyed da ya ce an yi satar gida kan kwallon ta shiga ragar Najeriya.

A duk lokacin da ake wasa na hamayya kowa kan zage damtse domin ya bayar da gudun mawarsa, kamar yadda Ronwen Williams mai tsaron ragar Afirka ta Kudu ya yi lokacin wasan duk da cewa tun farko Najeriya ta kasa amfani da bugun kusurwar da ta dinga samu da bugun tazara da sauran hare-hare, har sai a minti na 89 ta samu ta ci kwallo ta biyu.

Moses Simon wanda ya canji Ahmed Musa ne ya bugo kwallo daga kwana ta shiga da’ira ta 18 din Afirka ta Kudu daga nan ne, Williams ya shiga rububin ‘yan wasa domin ya naushi kwallon ta yi waje, sai aka yi rashin nasara ya naushi iska, kuma cikin sanyi William Troost-Ekong ya tura kwallo cikin raga.

Wasan ya kayatar matuka, kuma dukkan kasashen sun kusan kasa kai wa zagayen daf da karshe sakamakon kuskuren mai tsaron raga, amma na Williams shi ne mafi muni kuma duk da haka Super Eagles wadda take da kofin nahiyar Afirka karo uku ta hadu da Afirka ta Kudu a cikin rukuni a wasannin neman shiga gasar da Masar ke karbar bakunci.

Nijeriya ce ta ja ragamar rukunin, duk da nasarar da Afirka ta Kudu ta yi da ci 2-0 a wasan farko da tashi 1-1 a Afirka ta Kudu kuma haduwa da kasashen ke yi kan dora Najeriya a saman Afirka ta Kudu a karo da dama tun daga wasannin maza da na mata.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: