Connect with us

WASANNI

Rikici Ya Barke Tsakanin Arsenal Da Dan Wasa Koscielny

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Laurent Koscielny, yaki tafiya kasar Amurka tare da ragowar ‘yan wasan Arsenal domin fara buga wasannin sada zumunta  kafin fara kakar wasa ta bana.

A jiya ne dai kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta bayyana cewa dan wasan bayan nata, yaki bin ragowar ‘yan wasan kungiyar zuwa kasar Amurka domin fara buga wasannin sada zumunta sai dai har yanzu kungiyar bata bayyana dalilin yin hakan ba.

Wata sanarwa da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta fitar ta bayyana cewa tuni kungiyar ta kafa kwamitin ladabtarwa domin duba irin laifin da dan wasan yayi kuma zasu hukunta shi tare da cire shi daga matsayin kaftin din tawagar.

Dan wasa Koscielny dai ya damu da barin kungiyar kuma kamar yadda rahotanni suka bayyana tuni dan wasan ya shirya biyan ragowar kwantiragin daya rage masa a kungiyar wanda yake daukar fan dubu 90 duk sati.

Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa kokarin Arsenal na kin amincewa da sayar da dan wasan shine yasa yace bazai tafi tare da tawagar ‘yan wasan ba kuma tuni ya shirya karbar kowanne hukunci da kungiyar zatayi masa.

Kungiyoyin Bordeaud da Lyon da kuma tsohuwar kungiyarsa ta Marseille ne dai suke zawarcin tsohon dan wasan kasar Faransan, mai shekara 33 a duniya wanda kuma yayi ritaya daga bugawa Faransa wasa a shekarar data gabata.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: