Connect with us

SOYAYYA

Sirrin Soyayya Da Zaman Aure Da Dattijon Na Miji

Published

on

Sirrin soyayyan aure da dattijon namiji shi ne mace ta san cewa za ta yi kishi da matan da suka girmemata ne, wata kila kuma sun ma haifeta, irin wadannan mazan suna bukatar ganin mace da za su aura tana mutunta matansa na gida musamman uwargidan kamin ta shiga da kuma bayan ta shiga. Haka kuma duk da irin kaskantar da kansa da zai yi a gabanki ganin yana nemanki da aure kuma gashi zai iya kasancewa sa’an mahaifinki, yana da kyau ki mutuntashi kuma ki dauke shi da daraja ba wai kuma ki mai da shi wani boyi-boyi ba, saboda zai rufa miki asiri ya aure ki a matsayinsa na tsoho. Hakan zai ba ki martaba da daraja wajen ‘ya’yansa da kuma abokansa dama wasu masu sanya idanuwa game da soyayyan naku.

Irin wadannan mazan ba su cika kawo sako da kansu ba, akasari suka samu wani da suka aminta da shi ko kuma wani babba daga cikin yaran gidansu su aika ne wajen matan da suke so da aure. Anan sirrin maza irin wadannan dattijan shi ne, ki tabbatar ‘yan aiken su kina mutunta su, haka kuma kada ki yi wani abu, ko ki fadi wata kalma ko aikata wata dabi’a da zai iya kawo shakku a idanuwan dan aiken ko cusa masa wani kokwanto a zuciya yadda zai yi tunanin cewa maigidansa, ko mahifinsa ko kakansa zai auro mace ballagaza.

Da yake sun manyanta kuma sun saba da karauniya da ‘ya’ya da jikoki, kuma dadewarsu a duniya ya sa suka fahimce halaye na mata dai-dai gwargwado, mazan da suka manyanta masu neman aure maza ne da suke sha’awan ganin macen da za su aura kullum a cikin kwalliya, haka kuma suna son mace mai yawan shagwaba tabkar karamar yarinya ko kuma jika a gaban kakanta. Wani abun sha’awa da irin wadannan mazan shi ne, yana da wuyar gaske su nemi macen da za su aura da lalata koda kuwa suna da matsaniyar tsohuwar karuwace.

Kamar yadda kika yi hakuri a lokacin soyayyar neman auren ki da namijin da ya manyanta, haka za ki ci gaba da hakurin bayan kun yi auren.  Akasarin dattijawan maza dai yana da matukar wahala a rasa su da mace a lokacin da suke neman wani auren, haka kuma ana iya samun su da ‘ya’ya manya wasu lokutanma har da jikoki. Don haka duk macen da ta zabawa kanta zaman aure da irin wadannan mazan, to dole ne sai ta hada da gagarumin hakuri ko tana gida daya da sauran matansa ko kuma kowacce da muhallinta. Mafi yawan irin wadannan mazan da suka manyanta kuma suke bukatar aure, ba rashin jin dadin zama da tsoffin matansu ba ne ba sa yi, sai dai wasu loluta kamar yadda bincike ya tabbatar matan nasu na iya tsofar da ba za su iya gamsar da su ba a lokutan jima’i. Haka kuma wasu tsofin magidanta giyar kudi ne ke dibarsu su ji ko ba komai ai gara su samo wata mace mai dan galmi-galmi su aura, domin su burge abokansu. Wasu lokutan kuma abokai ne a tsakankaninsu suke yi wa ta yi ‘ya’yansu ga junansu.

Koma dai da wace hujja ko dalili mace ta yanke shawarar auren namiji da ya manyanta, babban sirrin zama da shi shi ne, ta tabbatar da cewa ba ta nuna wa matansa, ‘ya’yansa, jikokinsa, ‘yan uwansa da abokansa gadara da iyayin da za ta iya fiskantar matsala da su ba. Kamar yadda muka yi bayani a baya, a lokacin da dattijon na miji ya yanke shawarar auren mace, bai cika canza ra’ayi ba koda kuwa ya fahimci wani illa da macen da yake sonta da auren ba, haka kuma lokacin da ya aure mace bai cika barin wani matsala a tsakaninsu yana ba ta masa rai ba ganin cewa yana da kwarewar zama da mata da kuma sanin irin matsalolin mata da hanyar warwaresu ganin shima ana kawo irin wannan gabansa na ‘ya’yansa ko jikokinsa yana magace su.

Sai dai babban matsalar da macen da ta aure dattijon namiji za ta iya fiskanta a zaman aurenta da mijin nata shi ne, idan har ta sake wata matsala ya shiga tsakaninta da matan wannan mijin nata, ko kuma ‘ya’yansa. Wanda irin gallaza mata na karkashin kasa dana zahiri yana iya sanyawa ta gudu ta bar ladanta. Babban sirrin zama da irin wadannan magidanta shi ne, ki tabbatar da cewa babu raini a tsakaninki da matansa duk da yake yanzu abun da suke ji wajen dattijon ke ma kina danawa, haka kuma a wannan lokacin idan matansa marasa fahimta ne da tsoron Allah za ki ga abubuwa da dama da cusa bakin ciki da takaici tumma ba a ce kuna gida daya ba ganin su sun tasanma tsofa ke kuma yanzu kike more mijin nasu da su ci kurunciyan aure tare, amma ga shi yanzu sun zama ‘yan kallo.

Dole ki dauka cewa wannan matan da yanzu kike zaman kishiyoyi tare tamkar iyayen kine su, don haka duk wata bakar magana ko habaicin da za su yada miki ki kauda kunnenki tamkar baki ji ba. Haka kuma ki yi kokarin jawo wasu daga cikin ‘ya’yansu ko jikokinsu da kika fahimci cewa masu saukin kai ne da fahimta kusa da ke, domin kokarin nuna masu halin da kike ciki cikin hikima da dabara. Haka kuma ki tabbatar da cewa kin samu natsuwa sosai a duk lokacin da kika ga wani abu ba dai-dai ba a gidanki ganin zama da tsaffin mata a matsayin kishiyoyi, zama ne da mace take bukatr darasi a kansa ganin irin kissan da kisisina na gadar zare da irin wadannan matan za su iya shirya mace ta fada idan ba ta yi hankali ba.

Sirrin zama da magidantan da suka tsofa shi ne, a kullum ki dauke shi tamkar kina auren saurayi ne, kada ki kyamace shi ganin akasarin manyan magidanta ana iya samunsu da wasu halaye irin na tsofa. Haka kuma ki tabbatar da cewa yadda za ki yi soyayyar zaman aure da na miji mai karancin shekaru haka shi ma za ki yi da shi. Haka kuma ki cire a ranki cewa kina zaman aure ne da dattijon da ya ya yi sa’ar mahaifinki, saki jiki ki wahala ki yi soyayayyar zaman aurenki da mijin naki.

Sai dai kuma manyan matsalolin da mata suka fi fiskanta a lokacin zaman aure irin wannan shi ne na rashin samun haihuwa a wasu lokutan da kuma ishenshen kwaciya ta jima’i ga macen da ta ke da bukata da yawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: