Connect with us

TATTAUNAWA

Tattaunawa Da Janaf, Marubuciyar Littafin Ma’aikacin Kamfani

Published

on

Assalamu Alaikum kamar  yadda muka saba zakulo muku taurarinmu dominmu tattauna da su, a wannan makon ma Alhamdu Lillahi mun yi muku babban kamu tafe muke da daya daga cikin Tauraruwarmu, wadda za ku ji daga gare ta domin  Hausawa sun ce waka a bakin mai ita tafi dadi.

Sunana Jamila Umar wadda a kafar sadarwar zamani aka fi sani da Janaf

Da ni da masu sauraro za mu so jin takaitaccen tarihinki

Kamar yadda kuka ji da fari, sunana Jamila Umar, haifaffiyar garin zariya ce na yi makarantar firamare da sakandire dina a wata makaranta da ake kira “Contemporary Life School” da ke zariya.

Ahalin yanzu ina shekarar karshe ne a Kwalejin horas da malamai da ke Zariya wato, Federal Collage Of Education Zaria.

Me ya ba Janaf sha’awa a rayuwa har ta ji tana sha’awar fara rubuta littafi.

Gaskiya tun ina karama  rubutu da karatu yake a cikin jina, da su aka haife ni. Na kasance makaranciyar littafi kama daga na Hausa zuwa na Turanci. Na dade ina so ni ma na ba da tawa gudummowar zuwa ga al’ummata.

Na fara rubuce-rubucen littattafai a “Edercise book”  ina ajiyewa, har wata rana na ji ni ma bari na ba da tawa ‘yar gudummowar ta “online”. Wannan shi ne a takaice.

Ya kika ji da kika tsinci kanki a online?

Kwarai gaskiya da shi na zo duniya don tun ina karamata abin ke burge ni.

To a zahirin gaskiya na ji wani daban, saboda na zo wani guri ne na daban mai dauke da mabambamtan al’umma, masu bambamci ra’ayi. Amma duk da haka na maida hankalina kan Abin da na saka a gaba

Sai dai duk da haka na ji ni cikin farin ciki mara misaltuwa da Allah ya ba ni ikon isar da nawa sakon ta hanyar wayar sadarwa.

Ko zan iya sanin da wace marubuciya kika fara haduwa wadda ta taimaka miki ko na ce ta sa ki a hanya?

Wadda na fara sani a marubutan online kuma ta ba ni shawarwari masu kyau ita ce. Khadijat Beebeen Masoya. Bayan ita sai Aysha Sada Machika, a gaskiya wadannan bayin Allah sun min komai babu Abin da zan ce musu sai godiya da fatan gamawa lafiya, don da shawararsu da gudummowarsu a kaina na kawo yanzu har ake damawa da ni a duniyar marubuta online.

Za mu iya sanin ko wane littafi kika fara rubutawa online.

Littafin da na fara rubutawa shi ne Ma’aikacin Kamfani a kan me kika rubuta shi, ina nufin me ya kunsa. Labarin ma’aikacin kamafani ya kunsa yadda wasu mazan suke daraja aikinsu fiye da iyalansu ba su iya ba su dukkan hakkinsu wanda ya rataya awuyansu, sun fi maida hankali ga yadda za su juya biyar ta koma goma. Har hakan yakan jawo su matan su fada wata harkar banza wanda ba su da zabi.

Zuwa yanzu littafi nawa kika rubuta littafi uku kachal na rubuta a online

Muna son sanin sunansu cikin ukun nan wane kika fi so a cikinsu

Maganar gaskiya na fi son Nazir, Saboda shi ya fitar da ni sosai wanda ma bai san Janaf ba ya sanni. Har da wasu marubutan din da ban sani ba, sun kulla kawance da ni ta dalilin Nazir.

Wane  kalubale kika samu tun daga lokacin da kika fara rubutu online zuwa yanzu don ko na san komai ba a rasa kalubale.

Tabbas ba a rasa ba, sai dai ba wasu kalubale ba ne na a zo a gani. Kin san komai za ka yi a rayuwa ba ka rasa kalubale.To hakan ta kasance a wurina.

Wace nasara kika samu domin ita ma na san ba a rasawa

Tabbas nasara kam akwai, na samu nasarori da dama ta harkar rubutu babu Abin da zence sai godiya ga Allah. A cikin Nasaran nahadu da mutane wanda ko a mafarki ban taba zaton zan hadu da su ba kuma har alherinsu ya iso gare ni ba. Gaskiya babu Abin da zan ce sai hamdala.

Kwarai ma kuwa yana kwanyata littafin da na fara karantawa shi ne Babbar Illa, na Habiba Iman Ikara.Shi ne lttafin da na fara karantawa.

Wace marubuciya ta fi burge ki?

Marubuciyar da ta fi burge ni ‘yar gida ce wato Zulaihat Sani Kagara Da Halima Abdullahi Kofar Mashi. Abin koyi ne a gare ni gaskiya.

Wace marubuciya ce take burge ki har kike sha’awar ki taka irin matsayinta a rayuwa?

Ita din ce dai, Zulaihat Sani Kagara.Gaskiya tana burge ni matuka kuma ina fatan na taka mtsayin da ta kai a rayuwarta.

Me kika fi kauna a rayuwa

Abin da na fi kauna a rayuwata su ne iyayena, su ne dukkan ababen kaunata da farin cikina.

Me kika fi so a rayuwarki?

Tab dijam ai gaskiya kudi fa abin so ne.

Wace irin kyauta kika fi son a yi miki?

Kyautar kudi mana. Ai kudi kawai na ji an ce to Jami ga wannan, a dan kara. In amsa ina fadin kuma har da dawainiya bakina a washe. Ai ya fi min komai dadi.

Wane irin abinci kika fi so?

Shinkafa da wake da mai da yaji. Kina ba ni wannan kin gama mun komai.

Wace irin tsaraba kika zo wa masoyanki da ita?

Na zo musu da tsarabar Uwar Mijina. Labari ne mai dauke da sabon salo mai tafiya da salon zuciya Janaf ba ta taba yin labari wanda ita kanta yake tsuma ta ba irinsa. Zan sake shi da zarar na gama jarrabawa insha Allahu.

Da ni da masu sauraro za mu so mu ji shin Janaf na da aure ko kuwa ana hanya?

Maganar gaskiya Janaf budrwa ce ba ta da aure sai dai niyyar yi insha Allahu.

Me za ki ce game da kungiyarki ta IWA

Masha Allah har kinsa na ji dadi zuciyata ta yi sanyi Intelligent Writers Association, wallahi ba ni da bakin magana daya tamkar da dubu. Ko cikin dubun ma sai an tona. Zama cikinku wallahi nasara ce babba. Hadin kanmu kadai shi ke karamin sonka a raina. Abin da na sani shi ne ita din ta daban ce.Gaisuwa tare da jinjina gare ku masoyana.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: