Connect with us

Taskar Rayuwa

Bayan Karewar Wa’adin Shugaba Buhari, ‘Yan Arewa Ina Muka Dosa?

Published

on

Kafin shekarar 2002, lokacin da Shugaba Buhari bai tsunduma harkokin siyasar Nigeriya gadan-gadan ba, arewacin Nijeriya da ‘yan arewar ba mu da wani mutum fitacce, karbabbe kuma wanda ake yi wa zaton adaline irin Shugaba Buhari. Ban ce dai kuma babu kwata-kwata ba, sai dai wanda jama’a suke gani ya bayyana a zahirance shine Buhari.

Bayan shigowarsa harkokin siyasa gadan-gadan kuwa, sai talakawa musamman na yankin arewacin Nijeriya suka raja’a a kansa, yayinda suke sa ran idan Allah ya ba shi mulkin kasar nan, to zai fidda su daga akalla manyan matsalolin da suka addabesu.

A shekarar 2003, Shugaba Buhari yayi takara a jam’iyyar ANPP bai samu nasara ba, haka kuma a 2007 a jam’iyyar APP, nan ma ba a dace ba, 2011 a jam’iyyar CPC, nan ma ya fadi zabe. Sai a shekarata 2015 a karkashin jam’iyyar APC, Allah ya ba shi nasarar cin zaben Shugabancin kasar nan. Duk wannan lokacin da aka dauka, talakawan arewa suna tare da Shugaba Buhari a matsayin wanda suke sa ran zai cire musu kitse a wuta.

Hawan sa keda wuya, al’amura saka fara canzawa, manyan matsaloli irin na tsaro suka fara inganta, harkokin noma suka fara samun kulawa da tafi ta da, da dai sauran wassu al’amurran da ban.

Duk da cewar tsammanin ‘yan arewa daga wurin Shugaba Buharin bai cika ba, akwai abubuwan da ya kamanci aiwatar dasu kafin wa’adin nasa ya kammala a 2023, ya kamanta Shugaban ya kara kaimi wajen fidda ‘yan arewar daga mummunan talauci da suke ciki ta hanyoyin inganta ayyukan noma dana kiwo, wannan babban aikin da ya faro na RUGA (Rural/Urban Grazing Area) ya tabbata ya kammala kafin karshen wa’adinsa, abun da ya dace shugaban kasa ya yi a wannan lokacin ya toshe kunnensa daga masu sukar batun samar da Rugaye wa Fulani domin wannan abun zai taimaka wa arewa da zaman lafiyar Nijeriya gaba daya, don haka bai dace Buhari ya gaza aiwatarwa ba, yasar tafkin Chadi da ya ke ta magana akai, ya kamata ya fara koda ba zai kammala ba, manyan hanyoyin jirgin kasa su kammala, hanyoyi da ayyukan wutar lantarkin da ke arewa suma ya kasance sun kammala.

A dunkule abun da na ke son fitarwa kai tsaye wa shugaban kasa shine, ya dace shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma dan arewa ya duba kada ya mance da fata da kaunar da ‘yan arewa ke masa tun kafin ya zo kan kujerar nan, ya kuma duba kokarin da suka yi wajen tabbatar da ganin ya samu hawa kan kujerar nan ya share musu hawaye wajen gudanar da karin aiyukan da lallai za a ke tunawa da shi bayan shekarar 2023.

Daga ƙarshe kuma sai mu fara tambayar kawunan mu, Shin waye zai gajeshi ko kuma menene makomar mu Arewa/’Yan-arewar bayan wa’adinsa ya kare? Shin waye zai yi farin jinin da gaskiya da Buhari yayi daga arewar?

Dr. Salisu Dango

Ya aiko ne daga,

Yana, KH Shira, Jihar Bauchi,

2348032875677,

Sdango@ymail.com
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!