Connect with us

RAHOTANNI

Sarkin Bauchi Ya Bukaci Musulmai Su Rika Neman Ilimin Aikin Hajji

Published

on

Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji (Dakta) Rilwanu Sulaiman Adamu, a karshen mako ne ya ke mai bukatar al’ummar Musulmi da su rika neman ilimi da sani kan ayyukan hajji da zai taimakesu wurin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2019 da na sauran shekarun a kasa mai tsarki bisa yadda yake a tsare.

Sarkin wanda ke bayar da wannan shawarar a lokacin da yake kaddamar da wani littafi da aka wallafa kan aikin hajji ciki yaren Fulani da Hausa a garin Bauchi.

Dakta Rilwanu ya bayyana cewar aikin hajji Ibadace daga Allah a cikin rukunnai na ibado don haka akwai dokoki da ka’idojin gudanar da shi, yana mai shaida cewar akwai gayar muhimmaci kowani musulmi ya san ilimi aikin hajji da dokokin aikin hajji a kowani lokaci.

Sarkin wanda ya samu wakilcin daya daga cikin masu rike da sarautar gargajiya a jihar, Alhaji Ishak Ahmed Sambo, ya shaida cewar ta hanyar sanin ilimin aikin hajjin ne mutum zai samu damar gudanar da aikin hajji karbabbiya a lokacin da ya je Saudiya domin sauke farali.

“Idan mutum ya gudanar da aikin hajji da tsarkakken hali yadda Allah ya tsara, Allah ya yi alkawarin zai sanya shi a gidan Aljanna domin sakamakon wanda yayi aikin hajji karbabbiya kenan,” in ji shi.

Ya ce, aikata laifuka a lokacin gudanar da aikin hajjin babban laifi ne da hakan ka iya jawo Allah ya hukunta bawansa.

Sarkin ya ce ta hanyar neman ilimin aikin ne kowani mutum zai gane abun so da hani a lokacin gudanar da Ibadar hajji.

Ya yi fatan a gudanar da aikin hajji bana bisa nasara da kwanciyar hankali, sai yake jawo hankalin wadanda suka samu zarafin tafiya hajji a wannan shekarar da cewar su yi ayyukan da suke gabansu ba tare da shigar da wasu ayyukan da ka iya bata musu ibada ba.

Shugaba a wajen taron kaddamar da littafin, Alhaji Bello Muhammad Kirfi, ya jinjina wa sa’ayin mawallafin littafin a bisa kokarin da yayi wajen fito da aikin hajji a sauwake a cikin littafin nasa.

Ya ce, littafin zai taimaka sosai wajen baiwa maniyyata daman nazartar aikin tun kafin su je gudanar da shi a zahirance, ya tabbatar da cewar wani ilimi aka tara a cikin littafin wanda ya nuna farin cikinsa a bisa hakan.

Tun a farko, mawallafin littafin, Ustas Haruna Musa, ya shaida cewar littafin nasa ya kunshi muhimman bangarori guda biyu ne wanda yake koyawar da al’umma.

Ya ce, abu na farko shine littafin zai koyar da mutum tun kafin ya tafi aikin hajjin da kuma yadda zai gudanar da aikin idan ya samu kansa a kasa mai tsarki yayin gudanar da ibadar hajji.

Musa ya shaida cewar ra’ayin wallafa littafin ya zo masa ne domin kokarin gyara mafi yawan kura-kuran da al’ummar Fulani ke tafkawa a lokacin da suka je gudanar da aikin hajji, don haka ne ya shaida cewar littafin nasa zai taimaka wajen rage wannan matsalolin, don samun damar gudanar da hajji yadda ta ke a shari’ance.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!