Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Kungiyar Asiri Sun Farmaki ‘Yan Kungyar Sa-kai A Bayelsa

Published

on

Wasu mutane wadanda a ke kyautata zaton ‘yan kungiyar asirin ne da a ke kira da suna Greenlanders Confraternity, sun farmaki ‘yan kungiyar sa-kai lokacin da su ke bakin aiki a Yenagoa babbar birnin Jihar Bayelsa, inda su ka ji wa daya daga ciki mummunar rauni. ‘Yan kungiyar asirin sun raunata Mista Fred Godgift, inda su ke ta bugun bakinsa da bindiga a tashar Harbour da ke cikin garin Yanagoa da misalin karfe shida na safe.

A cewar mazauna yankin, ya kai kusan wata takwas ‘yan kungiyar sa-kai ba sa shiga yankin yin sintiri, sakamakon ‘yan ta’addan yankin. An bayyana cewa, ‘yan kungiyar asirin dauke da makamai da wasu muyagun makamai su ka mamaye ‘yan kungiyar sa-kai guda uku a tashar, inda su ka raunata daya daga cikin mutum ukun a kansa. Dan kungiyar sa-kai wanda a ka raunata, a yanzu haka ya na jiya a asibiti da ke cikin garin.   

Kwamandar ‘yan kungiyar sa-kai ta Jihar Bayelsa, Mista Tolumobofa Akpoebibo Jonathan, ya bayyana cewa, wannan farmaki ba zai hana taimaka wa jami’an tsaro ba wajen dakile ayyukan ta’addanci a lunguna da sako da ke cikin Jihar Bayelsa.

Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, domin an kira wayarsa bai dauka ba. Kuma har zuwa lokacin da a ke hada wannan rahoto bai mayar da sakon da a ka aika masa ba ta wayar salula.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: