Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Damke Mutum Biyu Da Kokunan Kan Mutane A Oyo

Published

on

A wannan makon ne, rundunar ‘yan sandar Jihar Oyo, ta gurfanar da wasu mutum biyu wadanda a ka damke da kokunan kan mutane a cikin garin Ogbomoso. Haka kuma, rundunar ta kara gurfanar da wani mutum wanda a ke zargin ya na da hannu wajen yin garkuwa da wata ‘yar kasuwa mai suna Misis Foluke Akinrinde, a cikin jihar. Majiyarmu ta labarta mana cewa, an yi garkuwa da Akinrinde ne lokacin da ta ke kan hanyarta ta zuwa kasuwa a makon da ta gabata.

Da ya ke gabatar da wadanda a ke zargi tare wasu ‘yan fashi da makami, kwamishinar ‘yan sandar jihar, Mista Shina Olukolu, ya bayyana cewa, an samu nasarar cafke Abdullahi Basiru da Adekola Martin, ranar 11 ga watan Yulin shekarar 2019, tare da kokunan kan mutane. Olukolu ya kara da cewa, an dai samu nasarar damke Ahmadu Musa, bisa zargin sa da hannu a wajen yin garkuwa da Foluke Akinrinde, a yankin Eruwa cikin karamar hukumar Ibarapa ta gabas ta jihar.

Sauran wadanda a ka gurfanar sun hada da wani mutum mai suna Tajudeen Olalere, mai gadin wata makaranta, wanda a ke zargin ya yi wa wasu dalibai guda shida fyade da kuma wasu mutum 46, wadanda a ke zargin su na da hannu a laifuka daban-daban da a ke aikatawa a cikin jihar.

Olukolu ya ce, “a ranar 11 ga watan Yulin shekarar 2019 da misalin karfe biyu na rana, tawagar ‘yan sandar yankin Ikoyi Ile/Ogbomoso wanda Sufeta Benjamin Olayiwola, ya ke jagoranta, su ka samu nasarar cafke Abdullahi Basiru da kuma Adekola Martin, dukkan su a yankin Oja Funi da ke cikin Jihar Osun tare da kokunan kan mutum biyu. Lokacin da a ka gudanar da bincike, ba a samu cikakken bayani a kan kokunan kai mutanen ba, amma har yanzu ana gudanar da bincike.

“A ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2019 da misalin karfe takwas na dare, wani mutum mai suna Sunday Akinrinde, da ke yankin Oke-Olaborin cikin garin Eruwa, ya kawo rahoto a ofishin ‘yan sanda da ke Eruwa cewa, a wannan rana da misalin karfe 3.30 na yamma, wasu masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matarsa mai suna Foluke Akinrinde, lokacin ta ke dawowa gida daga kasuwar Temidire, a yankin Sunbare da ke cikin garin Eruwa ta Jihar Oyo, a motar bas kirar Toyota mai lamba kamar haka KNR 670 DA. Kuma har yanzu masu garkuwan ba su kira waya ba, domin neman kudin fansa.

“Nan take rundunar ‘yan sanda sashen yaki da masu garkuwa da mutane su ka dauki mataki a kan lamarin tare da hadin gwiwar ‘yan kungiyar sa-kai da kuma mafarauta na yanki Eruwa, inda su ka samu nasarar ceto matar a ranar 2 ga watan Yulin shekarar 2019. Lokacin da a ka gudanar da bincike, an samu nasarar cafke daya daga cikin wadanda  a ke zargi mai suna Ahmadu Musa. Ya amsa laifin da a ke tuhumar sa, yayin da a ke farautar sauran wadanda su ke da hannu a cikin lamarin. “A ranar 27 ga watan Yunin shekarar 2019, an samu nasarar damke wani mai gadin makaranta, Tajudeen Olalere, bisa zargin sa da yi wa dalibai mata fyade na tsawan lokuta daban-daban.   
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!