Connect with us

LABARAI

Akwai Yiwuwar Mu Haramta Sana’ar Adaidaita Sahu A Kano – Shugaban KAROTA

Published

on

Ko shakka babu, alamu na nuna yiwuwar dakatar da ci-gaba da aiwatar da sana’ar Adaidaita a fadin Jihar Kano baki daya, amma dai yanzu tukunna ba za mu ce komai ba a kan wannan sana’a da Matasan wannan Jiha ta yi wa rubdugu. Dalili kuwa, Jami’an tsaro na nan suna ci gaba da aiki tare da yin bincike, da zarar sun kammala kuma za su tattaro mana bayanan da suka tace a kai, sannan mu kuma mu sake duba wa don yin hukuncin da ya dace ko dai a ci gaba da aiwatar da sana’ar ko kuma a hana yin ta kwata-kwata a fadin wannan Jiha ta Kano.

Wannan bayani ya fito ne kai tsaye daga bakin Hon. Dakta Baffa Babba Dan’Agundi, tsohon Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Kano sannan kuma sabon Shugaban Hukumar KAROTA, a yayin da yake zantawa da mane ma labarai, ciki kuwa har da Jaridar Leadership A Yau a Ofishinsa da ke Kanon, ranar Litinin din nan da ta gabata.

Hon. Dan’Agundi ya ce, da zarar Jami’an tsaro tare da sauran masu ßdaga nan ne za a san abin da ya kamata a yi, amma dai yanzu ba zan yi saurin cewa komai ba, saboda ka da na yi saurin azabarbabi ko riga-Malam-Masallaci. Kazalika, kowane irin mataki wannan Hukumar ta KAROTA za ta dauka a kan wannan sana’a ta Adaidaita sahu da kuma sauran abubuwan da hukumar ta ke da hurumi a kai wadanda doka ta sahale mata, sai nan gaba kadan za a ji matsayinta a kai, domin duk abin da zai kawo ci-gaban Kano ta fuskar tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali, shi ne abin da wannan hukumar za ta fi baiwa fifiko ba tare da tsoro ko shakkar wani ba, in ji Baffa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!