Connect with us

MAGUNGUNA A MUSULUNCI

Babbar Manufar Shaidanun Aljanu Ita Ce Raba Mutum Da Matarsa

Published

on

Shaidanun aljanu suna rudin ‘Yan Adam da rudinsu, shi ne ma Allah Ta’alah yake cewa ‘’Fadallaahuma bi Guruur.’’ Wato suka batar da su da rudani. Sannan idan ma ya yi auren, aljanu za su yi iya yinsu wajen ganin auren ya mutu, har ma su kan yi na su asirin su barshi a jikin mutum, su kuma basa zaune, saboda haka ko an yi karatu ma ba za a ji aljani ba, sais u rika zuwa jifa-jifa.

Shi ne Ibnu Kasir Dabari da Naisabuuri da Bagawi da Sa’adi, suka ce a cikin Tafsirinsu, cikin Suratu Bakara  ‘’Fa yata allimuna maayufarriku bihi bainal mar’i wa zaujih’’. Wato aljanu suna koyar wa yadda za a raba miji da matarsa, suka ce yana daga cikin babbar manufar Shaidanun aljanu su raba mutum da matarsa. Su kanyi amfani da sihirinsu su bata kyan mata a wurin mijinta, ko kuma su munana kyan miji a wurin matarsa.babban kaidin da suke yi wa ma aurata don su raba aurensu shi ne, su hana namiji ya iya biya wa matarsa bukatarta. Allah Ta’alah yana cewa ‘’Wamin ayatihi an khalaka lakum min anfisikum azwaja litaskunuu ilaiha waja ala bainakum mawaddatan warahmah’’wato yana daga hikimar Allah Ta’alah ya halitta maku matanku daga cikinku don ku samu nutsuwa, sannan ya sanya kauna da jinkai a tsakininku, wato kaunar juna miji yana sha awar matarsa da bukata. Wato an halitta mku matanku daga cikinku ba daga wata dabba ba.

mata tana son mijinta ya biya mata bukatarta shi ma yana son matarsa ta biya masa tasa bukatar. To amma akan samu rauni biyan bukatar juna a wurin kwanciya, imma dai namiji ya daina biya wa matarsa bukata tsahon lokaci, daga sai ta fara tunanin yadda za su rabu. Inda za mu kara gane hakan shi ne, Hadisin matar Rifata (RA) da ya zo a Bukhari da Muslim daga Nana Aisha (RA) ta ce ‘’Ja atilmar’atu Rifa’atal Kuraziyyu ila Rasulillahi SAW fa kalat Ya Rasuulallahi inni kuntu Rifa’atulKurazi fadalakani fabattu dalaakee fatazawwajtu ba adahu Abdurrahman bn Zubair, innama ma ahu mislu hudbatussabi, fatabassama rasulillahi SAW wa kaala; ‘’Turidina an tarja I ila Rifaa’atu, hatta ta zuuku Usailatahu waya zuulu usailataki’’

wato matar Rifa’atul kuraizi ta zo wurin manzon Allah SWA take cewa ni na kasanceina auren Rifa’atalKurazi, sai ya sake ni sakin da ya kai uku, saboda haka bayan n agama idda, sai na auri Abdurrahman bn Zubair (RA) to amma gabansa kamar lagwani yake, sai manzon Allah ya yi murmushi sannan ya ce, in kina son ki koma gidan mijinki sai kun dandani zumar juna.’’

To ku duba yadda wannan Sahabiya bata ji kunyar bayyana wannan lamari ba, kuma da zauna wurin wannan sabon mijin nata gara ta koma wurin na baya duk rashin zaman lafiyar da suke yi, wanda har ya kaisu ga rabuwa. Da ma Nana Aisha tana cewa ‘’Ni’mannisaa’ansar lam yamna ahum haya’u an yatafakkahna fiddin’’

wato ‘’Madalla da matan Madina, kunya ba ta hana su koyon addininsu.’’ Ita bata ji kunya bane, sabida tausayinsa ya ragu a zuciyarta, sanin haka da manzon Allah ya yi shi ya sa yake cewa ‘’Iza jama’a ahdukum ahluhu falyasdukhaa. Summa iza kadha hajatahu kabla an takdhi hajataha, Kaala yu’ujilha hatta takdhi hajatahaa.’’

Daga Anas mus’abu dan Abu Ya’ala Allah ya kara masa yarda ya ce ‘’Manzon Allah mai tsira da mincing Allah ya ce ‘’Idan dayanku  ya zo saduwa da matarsa, to ya gaskantar mata, sannan idan ya yi Inzaali, kafin ta yi, to kada ya barta haka sai ita ma ta yi. Wato dukkaninsu sai samu biyan bukata. Nan da Manzon Allah yake cewa ‘’Falyasadukha’’ Malamai suka ce k aba da himma ka yi da karfinka, ka bata wahala, don su wahalar suka fi so.

To amma su shaidanun aljanu da yake duk sun san irin wannan ilmin, saboda suna da ilmi kamar yadda Ikrama ya ruwaito daga Ibnu Abbas acikin Tafsirin Kurdabi cewa ‘’Wastakbar wakaana minalkafirin’’ to shi ne, sai su yi kokari su hana jin dadin jima’i, tunda su kan iya hana gaban namiji ya yi girma yadda ya kamata. Domin suna yawo a cikin jijiyoyin jikin mutum kamar yadda jini yake yawo. Shi dai gaban da namiji tsahon yatsu 12 to haka ake so, ko yayi ‘yan yatsa 10, amma ba a so ya yi kasa da ‘yan yatsu 8 wato danka biyu. Kaurinsa kuwa ya kai nadi biyar zuwa shida, wanda yake da kasa da haka, sai an kara masa tasayi da kuma kauri, saboda wasu matan ma su kan so sama da yatsu biyar zuwa shida.

Saboda haka su wadannan aljanu sais u haifar da matsanancin sanyi da toshewar zuciya, sannan su hana kwaranyar jini zuwa gaba. Saboda haka sai a samu kankatar gaba, ka ga ke nan ba zai iya biya wa matarsa bukata ba., don ba zai iya gamsar da ita ba. duk da yake wannan matsalar akwai wadda ba ta aljanu bace, to amma duk akwai maganinsu a likitancin Manzon Allah SAW.

Inda muka kara gane wannan makircin na aljanu, a lokacinda mu ka yi nasiha ga maza, muka ce da maza su gyara jikijnsu,ya kasance ko wane lokaci a shirye suke, yadda duk yadda matanzu suka kai ga bukata za su iya biya masu bukatarsu koda Ka ara ce wato mai tsananin zurfin gaba, kuma koda Harija ce wato mai tsananin sha’awa da rashin gajiya.

Sai muka samu maza da yawa suka zo akan a kara masu girman gabansu, har da wadanda suke (Innini) ne amma wasu sais u zo su ce bai karu ba, kai har ma akwai wanda ya ce ya sayo wani daga Turai, wanda ya ga an gwada da gabansa ya yi, amma shi bai yi mas aba. da muka bincika sai muka samu cewa wasu da wasu kuma da sihiria jikinsu, wasu kuma aljanu, wannan duk yana cikin kaidin aljanu don su raba aure ko su raba aure, tunda akwai wanda muka yi masa magani aka kara masa, sannan ya yi aure, kuma ya kai shekara 46. Saboda shi ya san gabansa dan mitsitsi ne bai kai dan yatsa ba, haka su kan yi su haifarwa namiji saurin kawowa, don kada ya biya wa matarsa bukata, daga nan sai aure ya rabu ko ta kama bin wani a waje, ko kuma ta bi wata hanyar da za ta rika biya wa kanta bukata.

Shi ya sa Manzon Allah y ace; ‘’Bayan mutum ya kawo, to kada ya daina har sai matarsa ita ma ta kawo’’ wato ita mata biya bukatarta. To shi saurin kawowa akwai na aljanu akwai na ciwo, kuma ko wanne Malamai cewa suke sai an magance shi, don abi umarnin Manzon Allah SAW. Shi ya sa Bagawi a cikin Tafsirinsa cikin Suratu Bakara Aya ta 270 yake cewa Shaidanun aljanu su kan doki mutum su hana shi jin dadin jima’i, kuma shi ya sa ma Manzon Allah SAW ya ce; ‘’Idan dayanku zai yi jima’i ya ce, ‘’Allahumma Jannubna minasshaidani, wajannubisshaidani maa razaktana’’ don yayin saduwa aljanu su kan zo. Kuma a cikin littafinsa (Arrahmatu fiddibbi) yake cewa ‘’duk wanda ya kasance ya zo saduwa da matarsa, ko kuma kafin ma ya fara ya kawo, to akwai sihiri a jikinsa, kuma mun san Sihiri baya yiwuwa sai da aljanu.

Ya ‘yan uwa mu sani gaskiya anan cutar da mata sosai, don wani daga nan abin yake kaiwa ga mutuwar aure, wani kuma daga nan sai ya kasance wani lokaci ma in an zo saduwar ma gaban ya ki aiki. Yadda z aka gane irin wannan matsalar shi ne; Malamai suka ce, ‘’ Duk wanda ya  yi Inzali kasa da minti 15 to bai biya wa matarsa bukata ba, wando ko ya kai minti 30 ba za a yabe shiba ba zakuma a zarge shi ba. wanda ko ya kai awa daya yana yi, wannan ya fara zama namiji.

Amma abinda likitoci suke cewa shi ne, miji ya san lokacin da matarsa take kawowa, bayan ta kawo sai ya kara minti kamar 15 sannan ya kawo, ko kuma su kawo tare. Akwai wata mace da aljanu suka raba aurensu da mijinta ta wannan hanyar a Saudiya, mijinta Soja ne, sai suka kashe sha’awarsa, saboda haka bay a iya saduwa da ita, ita kuma suka kara sha’awarta yadda a cikin dare har kuka z aka ji tana yi, suka yi neman magani har kusan shekara 7, muka hadu da shi a wurin karatu da mku yi a gaban Sudais, inda na ji matsalolinsa, na zo na fara yi masa aiki, aljanun wurin suka bayyana mana komai, sannan aka samo wasu aljanu suma suka tabbatar, suka ce ai asiri suka yi suka ajiye a karkashin gidan, kuma suka tafi nasu wurin, saboda haka ko an yi Rukuya ma ba za a ji su ba. ‘’Alhamdulillahi La haula walakuwwata illabillah’’ yanzu sun samu lafiya sun ci gaba da rayuwarsu. Allah Ta’alah yana cewa ‘’Innasshaidana kana lil insani aduwwan mubina’’
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!