Connect with us

LABARAI

Dukiyoyin Haram Ke Rura Wutar Ta’addanci A Afrika –Shugaba Buhari

Published

on

… Ya Nemi Jami’an Tsaro Su Dau Mataki

A ranar Alhamis ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga hukumomin tsaro a Afrika musamman jami’an tsaro masu binciken sirri da su kara zage damtse a kan kwararar dukiyoyin haramun.

Ya danganta yawaitan dukiyoyin haramun da karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta daga masu cin riba daga irin wadannan dukiyoyin na haramun.

Buhari ya yi wadannan kalaman ne a lokacin da yake bude taro na 16 na kwamitin jami’an tsaron sirri na Afrika (CISSA) a Abuja.

A cewar sanarwar da mai taimaka wa Shugaban kasan a kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina,ya fitar Buhari ya ce, ci gaba da kuma zaman lafiya a nahiyar ta Afrika, duk yawan kwararar dukiyoyin haramun din da kimar su ya kai dalar Amurka bilyan 60 a duk shekara ya gurgunta su.

Shugaba Buhari ya yi nuni da cewa, taken taron, “Hada-hadar dukiyoyin haram daga Afirka da kuma tasirinta ga tsaron kasa da ci gabanta” shi ne mafi cancanta a daidai wannan lokacin, sai ya bukaci masu ruwa da tsaki daga sasan hukumomin tsaron masu binciken sirri na kasashen Afrikan 52 da su samar da wani bagire da zai samar da dubaru a kan yanda za a dakile duk wata dangantaka a tsakanin aikata laifi da zaman lafiya a nahiyar tamu.

Shugaba Buhari ya kuma kalubalanci taron da ya samar da matakan da za su tabbatar da masu aikata laifuka ba su kusanci dukoiyoyin al’umma ba.

Shugaba Buhari ya ce ana bukatar daukan kwararan matakai domin magance barazanar masu aikata laifi, ya yi nuni da cewa, duk wata hanya ta kauce wa doka da take taimakawa masu cin dukiyoyin al’umma ta hanyoyi daban-daban da suka hada har da kwararar dukiyoyi ta hanyar haramun ya zama wajibi a yake su sosan gaske har a kawar da su.

A cewar shi, “matsayina na jagoran yakar cin hanci da rashawa a nahiyar Afrika ne ya kara nuna mani inda hadarin girman kwararar dukiyoyin haramun din ya kai a nahiyar tamu.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!