Connect with us

FILIN FATAWA

Ko Ya Halasta Na Raba Gadona Kafin Na Mutu?

Published

on

Tambaya:

Slm,malam don Allah ina da tambaya da fatan za’a amsamin, wai mutum zai iya rabawa iyalansa gadansa kafin yamutu wai hakandin ya halatta? Na gode.

Amsa:

To dan’uwa malamai suna cewa hakan bai inganta ba, saboda dalilai, ga wasu daga ciki :

1. Hakan yana daga cikin gaggauta abin da Allah ya jinkirta, saboda Allah ya sanya rabon gado ne, bayan mutuwa.

2.  Zai iya yiwuwa daya daga cikin  iyalan nasa ya mutu kafin shi, ka ga sai a samu kwan-gaba kwan-baya.

3. Yana iya jawo hassada saboda daya daga cikin magadan zai iya yin kasuwanci da gadon da aka ba shi ya samu riba mai yawa kafin magajinsa ya mutu, wanda hakan zai iya kawo hassada tsakanin magada, don za su ga da ba’a yi gaggawar rabawa ba da ya kasance daga cikin rabonsu.

4. Yana daga cikin sharudan gabo tabbatar da mutuwar  wanda za’a gada .

Allah ne mafi sani.

Babu Bambanci Tsakanin Wiwi Da Giya A Haranci

Tambaya:

Assalamu Alakum. Malam ina da tambaya kamar haka,shin tabar wiwi tana daukan dukkanin hukunce hukuncen da suka hau kan giya (barasa)ko kuwa akwai banbanci.Dafatan zanga amsan wannan tambaya a Zauren Fikhu. Na gode.

Amsa:

Wa’alaikum assalam, mutukar ta amsa sunanta na WIWI kuma tana bugarwa, tabbas za dauki dukkan hukunce-hukuncen giya na haramci.

Annabi (SAW) yana cewa “Dukkan abin da yake sanya Maye giya NE, kuma dukkan giya haramun ce” kamar yadda Nasa’i ya rawaito a hadisi ingantacce, wannan sai ya nuna haramcin shan WIWI da duk abin da yake sanya maye.

Allah ne mafi Sani.

Fatawar Rabon Gado (11)

Gadon Mata-Maza!

Tambaya

Assalamu alaikum, malam idan mutum ya mutu ya bar mata-maza da ‘yan’uwa, yaya rabon gadon zai kasance ?

Amsa:

Wa alaikumus salam To dan’uwa mata- maza shi ne wanda yake da al’aurar mace da ta namiji, kuma ya kasu kashi biyu

1. Akwai mara rikitarwa, wato wanda aka gane inda ya fi karfi, kamar ya zama yana haila, kaga za’a riskar da shi da mace wajan rabon gado, ko ya zamayana fitsari ta al’aurar namiji, to wannan hukuncinsa hukuncin namiji a wajan rabon  gado haka nan idan ya zama yana da gemu da gashin baki.

2. Mai rikitarwa, wannan shi ne wanda akakasa gane inda ya fi karfi, kamar ya zama yana fitsari ta ala’aura biyu, kuma ba wanda yafi fitowa da karfi ko da yawa a cikinsu, ko kumaya zama yana da gemu, kuma yana haila. Idan har mata maza ya balaga ba’a gane inda yafi karfi ba, to za’a ba shi rabin gadon mace ne, da rabin gadon namiji. Duba : Attahkikatalmardhiyya fi-mabahithil-fardhi yya shafi na 206.

Allah ne mafi sani .

Hukuncin Canza Wuri Bayan Sallar Farilla Kafin Sallar Nafila

Tambaya:

Menene asali ko dalili idan mutum ya idar da salla zai yi nafila sai naga ya dan matsa baya ko gaba daga inda yayi sallarsa, akwai hadisi ne akan haka?

Amsa:

To dan’uwa Akwai hadisin da yake nuna haka, saidai wasu malaman hadisin sun raunana shi kamar Bukhari a sahihinsa, a hadisi mai lamba: 848, amma Albani ya inganta shi saboda yawan hanyoyinsa, a cikin littafin Sahihu sunani abi-dawud 3\178.

Sai dai, malamai suna cewa: ana so ayi hakan saboda gurare da yawa su yi ma mutum shaida. Amma abin da ya fi ga liman shi ne canza wuri, saboda abin da aka rawaito daga Aliyu – Allah ya kara masa yarda- yana cewa: “Yana daga cikin sunna, liman ya canza wuri idan zai yi sallar nafila” wannan yasa Imamu Ahmad ya karhantawa liman ya yi nafila a inda ya yi sallar farilla, don kar a zaci sallar ba ta kare ba.

Fathul-bary 2\335.

Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado (12)

Tambaya:

Assalamualaikum. Malam tambaya che kamar haka : mutun ne ya mutu ya bar uba da uwar uwa da yaya maza da mata yaya rabon zai kasanche Allah kara basira.

Amsa:

Wa alaikum assalam To dan’uwa za’a raba gida shida, a bawa uba kashi daya, sai Uwar uwa kashi daya, sai a bawa ‘ya’yan ragowar, su raba, na miji ya dau rabon mata biyu Allah ne mafi sani.

Mijina Ya Sake Ni Da Danyan Goyo, Yaya Iddata ?

Tambaya:

Assalamu Alaikum, Dr. Tambayace- mace mijinta ya saketa bayan ta haihu da danyen goyo. Ya iddarta zata kasance? Allah ya karawa Dr. Ikhlasi.

Amsa:

Wa alaikum assalam. Za ta jira jini uku Kamar yadda aya ta (228) a Suratul Bakara ta tabbatar da hakan, ba za ta yi aure ba har sai ta kammala su, Allah ya kara mana iklasi a duka lamuranmu.

Allah ne mafi sani.

Bambanci Tsakanin Maniyyi Da Maziyyi Da Kuma Wadiyyi

Tambaya:

Assalamu alaikum. Don Allah malam ina so a bambance min tsakanin wadannan ruwaye, wato maniyyi da maziyyi da wadiyyi, saboda nima tambaya ka yi min akan haka!

Amsa:

Wa alaikum assalam. To ‘yar’uwa Allah ya datar da ke, ga abin da ya sawwaka:

1. Maniyyin namiji : ruwa ne mai kauri FARI wanda yake fitowa ya yin babbar sha’awa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin kamshi kwai. Maniyyin mace : ruwa ne tsinkakke, mai fatsi-fatsi, wani lokacin kuma yana zuwa fari, wanda yake fitowa ya yin babbar sha’awa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, sannan za ta ji tsananin sha’awa da kuma dadi lokacin da ya fito, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin kamshi kwai, kuma za ta ji sha’awarta ta yanke bayan fitowarsa. Hukuncinsa shi ne : yana wajabta wanka.

2. Maziyyi: Ruwa ne tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha’awa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kake so, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike sha’awa, haka nan yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi ba ya sa sha’awa ta tafi, kuma wani lokacin ba’a sanin ya fito. Malamai suna cewa : Maziyyi ya fi fitowa mata, fiye da maza, lokacin da maziyyi zai fitowa namiji azzakarinsa zai mike. Hukuncinsa shi ne a wanke farji gaba daya, da kuma inda ya shafa, kuma a sake alwala.

3. Wadiyyi: Wani ruwa ne mai kauri da yake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yi ba, yana fitowa ga wadanda suke fama da gwauranci ko wadanda suka yi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace. Yana daukar duka hukunce- hukuncen fitsari.

Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado (13)

Tambaya:

Assalamu Alaikum Warahmatullah. Malam mutum ne ya rasu, ya bar mahaifiyarsa da mata biyu da kuma ‘ya’ya mata da maza. Ya rabon gadonsa zai kasance? Allah ya saka maka da alheri malam.

Amsa:

Wa alakum assalam To dan’uwa za’a raba dukiyar gida 24, a bawa mahafiyarsa kashi 4, sai abawa matansa kashi 3 su raba, sai a baiwa ‘ya’yansa ragowar., su raba a tsakaninsu, duk namiji zai dauki gadon mata biyu.

Allah ne mafi sani .

Shekara Daya Mijina Bai Sadu Da Ni Ba, Mece Ce Shawara?

Tambaya:

Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah yasamu dace. Malam don Allah ina son nasan matsayin aurena shekara daya mijina be kusanceniba alhalin muna tare kuma dukkanin mu muna lafiya. Nagode

Amsa:

Wa alaikum assalam. Auranku ingantacce ne,, amma zai yi kyau a kira magabatanku a tattauna matsalar, tun da saduwar ma’aurata ginshiki ne na Zamantakewar aure, wanda rashinsa yana kai ma’aurata zuwa saɓon Allah. In har ba ku cimma matsaya ba, bayan zama da magabata kina iya kai shi Kotu alkali ya muku hukunci, Saboda a musulunci bai Halatta miji ya kauracewa matarsa ba sama da wata (4) kamar yadda aya ta (226) a suratul Bakara ta tabbatar da haka.

Allah ne mafi sani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!