Connect with us

LABARAI

Tsarin Noman Fadama Na Kano Ya Fi Duk Na Sauran Fadin Nijeriya Inganci – Dakta Gawuna

Published

on

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Nasiru Yusif Gawuna, ya bayyana shirin Noman Fadama na Jihar Kano da cewa, shi ne mafi inganci idan aka kwatanta shi da sauran na fadin kasar nan, musamman idan aka yi la’akari da yadda shirin ke kara habaka tare da inganta amfanin da Manoma a Kano ke nomawa.

Dakta Gawuna, ya bayyana haka ne a ranar Alhamis din da ta gabata, lokacin da yake karbar bakuncin Shugabannin Kwamatin tsarin Bankin Duniya mai lura da samar da abinci tare da tallafin inganta harkokin rayuwar al’umma (Appeal), wadanda suka ziyarce shi  a Ofishinsa da ke Fadar Gwamnatin Jihar Kano.

Har ila yau, ya ci gaba da cewa, wannan nasara ta samu ne sakamakon tallafin da Gwamnatin Dakta Abdulahi Umar Ganduje, tare da hadin gwiwar Jami’an gudanar da wannan shiri a nan Jihar Kano, wanda shirin ya kawo gagarumin ci gaban matsakaitan Manona.

“Ina sane da yadda wannan Gwamnati ta jajirce tare da hada karfi guri guda domin tabbatar da gudanar wannan shiri a Jihar Kano, ba tare da tsoro ko kunbiya-kunbiya ba. Ko shakka babu, Noman Fadama a wannan Jiha ta Kano, ya haura na dukkanin sauran Jihohin Nijeriya inganci.”  A cewarsa.

Haka zalika, a cewar Mataimakin Gwamnan, idan aka yi la’akari da wani bangare da tallafin ya baiwa  gagarumin goyon baya a Jihar, shi ne gudunmawar Motocin Noma guda

takwas da Gwamnatin Kano ta damkawa mahalarta taron domin saukaka musu harkokin Noma.

Sannan ya kara da cewa, Noma don samun riba ya samu kulawar da ta kamata kasancewarsa guda cikin tsarin da ke taimaka wa Manoma ta fuskar inganta harkokinsu a Jihar Kano. Haka kuma, ya jaddada cewa, mata da Matasan da suka rungumi irin wannan Noma na samun gagarumin ci gaba wanda zuwa wannan lokaci kaso 85%  na wadanda suka halarci wancan

shiri na amfana da abubuwan da suka koya, in ji shi.

Mataimakin Gwamnan ya kuma bayyana cewa, akwai wasu hanyoyi masu inganci wadanda Gwamnatin Kano ke da ruwa da tsaki da su, wadanda suka hada da Noman Shinkafa , Alkama da kuma Tumatir da sauran su. Ya ce zuwa yanzu Jihar Kano, ta zabi ci gaba da kaddamar da Noman Shinkafa a lokacin rani karkashin shirin nan na Ancho Borrowers, wanda Jihar Kanon  ke da tulin Manoma wadanda suka yi rijisata. Inji Gawuna.

Haka zalika, ya tabbatar wa da tawagar tabbacin wannan Gwamnati na tallafawa tare da bayar da dukkanin goyon bayan da ake bukata, musamman a kokarin da Gwamnatin Kano ke yi na kara habaka tattalin arziki ta fuksar Noma. Sannan dukkanin sauran batutuwa kuwa, Gwamnatin Jihar Kano na da kyakkyawan shirin hada hannu da wannan Hukuma domin samun kyakkyawan sakamako.

Har ila yau, shi ma a nasa jawabin, jagoran tawagar Bankin Duniya a kan harkokin inganta Noma tare da inganta rayuwar al’umma, Dakta Adetunji Oredife cewa ya yi, sun zo Kano ne domin duba shirin don neman ci gaba da samun tallafin Gwamnatin Kano, domin kara inganta harkokin shirin.

“A lokacin da na zo, na tarar da tsare-tsaren halin da ake ciki, wanda na fahimci cewa, lallai akwai ingantacce harsashi da aka dora wannan shiri a kai,  musamman wasu gine-gine da aka samar, Adetunji ya kuma bayyana cewa, wannan shiri na Appeal shiri ne wanda ya zo daidai,

musamman ganin yadda aikace-aikacen da ake gudanar da su cikin basirar da aka samu daga tallafin farko domin dorewar amfanin Manoman.

Don haka, za mu ci gaba da inganta hanyoyin samar da abinci zuwa mataki na

gaba, haka kuma mun samu nasarar warware matsaloli tare da taimaka wa wannan shiri wanda ake gudanarwa ahalin yanzu, sannan babban kalubalen da ke fuskantar wannan tawaga shi ne, tabbatar da abubuwan da aka faro tare da mayar da hankali domin samun tallafi  don ci gaban shirin nan da shekaru masu zuwa”, in ji shi.

Adetunji, ya kara da cewa, batun inganta rayuwar al’umma kuwa, abubawa ne masu yawa ga

Jihar Kano da ma Tarayyar Nijerirya baki daya, wanda hakan ne ke nuna cewa,  lallai

akwai gagarumin aiki a gaban Gwamnati wanda ya kamata a magance ba kuma harkar noma kadai ba, har ma da sauran bangarorin da suka shafi mata da kuma Matasa. Kamar Yadda Darktan yada labaran Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Hassan Musa Fagge ya shaida wa Jaridar Leadership A Yau Juma’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!