Connect with us

SOYAYYA

Mace Ta Fara Koya Min Soyayya

Published

on

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU ASABAR. Da farko dai sunana Yusuf Shuaibu, kuma ina farin cikin da bude mana wannan shafi mai albarka, domin bayyana irin soyayyar da muke gabatarwa ko kuma wacce muka gudanar a baya. Lallai ni dai a rayuwata ta duniya, na fara soyayya ne tun lokacin da na zama cikakken saurayi mai hankali. Yadda lamarin ya kasance kuma shi ne, na samu jarabawa mai yawa a kan soyayya. Ni mace ce ta fara koya min soyayya, inda a wannan lokaci soyayya ta sa ba na ko iya cin abinci mai yawa da na ci kadan sai in ji na koshi, ga tunani mai yawa wanda ya janyo har sai da na rame kamar wanda ya yi jinya.

Na fara soyayya da wata yarinya mai suna Zainab. A yayin gabatar da soyayyana a gar eta, na yi amfani da salo mai karsashi, wato sai da na gama jan hankalinta da ra’ayinta a kai, kafin na bayyana mata soyayyana. Lallai furta Kalmar amincewa na soyayya tun da farko abu ne mai matukar wahala ga mace, sai dai tun da haka ni kam na samu wannan lamari cikin ruwan sanyi. A lokacin da kake kokarin gano matsayinka a zuciyar budurwarka a kan shi tana son ka ko akasin haka, akwai bukatar ka nazarci wasu abubuwa a game da ita. Kadan daga ciki sun kasance kamar haka, matukar mace tana son ka, to za ta kasance mai karbar shawararka duk lokacin da ka ba ta, kuma za ta kasance mai son abun da kake so. Wannan dalidai su suka tabbatar min da abin da ta furta min tun a farkon lamari. 

Mun shaku sosai da wannan yarin, tana matukar so na, abun takaicin shi ne, lokacin da muka shaku da ita kamar ba za mu iya rabuwa ba, sai kuma iyayanta suka auran da ida ga wani mutum wanda ba ta ma yi soyayya da shi ba. Wannan lamari ya sa na shiga cikin damuwa da tashin hankali mai yawa. Na kasa cire soyayyarta a cikin zuciyana, inda har yanzu da nake yin wannan rubutu, ina jin soyayyarta a cikin zuciyana. Saboda a lokacin da muke ganiyar soyayya da ita, kullum zai mun ga junan mu. Tana matukar cin maganana fiye da na iyayenta. Kifin soyayyarta ya fita daga cikin zuciyana, sai da na yi ta rokon Allah a kan ya cire min son ta a cikin zuciyata. Ina a yanzu kuma kamar an yi ruwa an dauke. Sai dai har yanzu ba yi aure ba, ina duba wacce za ta iya maye gurbinta a cikin zuciyata.

Abangare daya kuma soyayyar ta sani farinciki tare da annashuwa, ban samu wani bacin rai ba har sai da na kwashe tsawan shekaru masu yawa. 

Ni dai a lokacin da na fara soyayya kenan.

Sakon soyayya daga dan uwanku Yusuf Shuaibu, Kaduna.

08034980391
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!