Connect with us

RAHOTANNI

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Tanko A Matsayin Babban Alkalin Nijeriya

Published

on

A shekaran jiya ne aka tabbatar da Mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin Babban Alkalin Nijeriya (CJN).

Tabbatar da shi din ya biyo bayan amincewar da majalisar dattawa ta yi masa a ranar Larabar da ta gabata.

Babban Mai shari’a Tanko, ya kasance a matsayin mai rikon mukamin CJN tun a ranar 25 na watan Janairun wannan shekarar jim kadan bayan da aka dakatar da Justice Walter Onneghen daga mukamin bisa zargin tafka laifukan rashawa.

Shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar Alhamis din makon jiya ne ya tura wasikar neman amincewa da Justice Tanko a matsayin cikakken CJN.

Shugaban kasar a cikin wasikar bukatar tasa, ya shaida cewar neman tabbatar da Tanko din ya biyo bayan shawarar yin hakan ne da hukumar NJC ta bayar.

Wasikar ta kunshi bayani kamar haka, “Nadin babban Alkalin Nijeriya a bisa sashi na 231 (1) da ke kundin tsarin dokokin Nijeriya na 1999 wanda aka yi kwaskwarima, ya bai wa shugaban kasa iko da damar nada babban Alkalin kasa a bisa shawarwarin hukumar kula da harkokin shari’a (NJC) gami da neman tabbatar da nadin daga majalisar dattawa,” A cewar wasikar.

Don haka ne ya nemi majalisar dattawan ta amince da bukatarsa ta nada Justice Tanko a matsayin Babban Alkalin Nijeriya, inda majalisar ta kuma amince da wannan bukatar bayan amincewa da tantance shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!