Connect with us

KASUWANCI

Nijeriya Za Ta Fara Sayarwa Kasar Indiya Mai

Published

on

Shugaban rukunin kamfanin na NNPC, Mele Kyari ya sanar da cewa zai fara sayarwa da kasar Indiya kashi goma na man fetur.

A cewar Mele Kyari kamfanin ya yi hakan ne don taimakawa Indiya ta warware matsalar makamashi da ta ke fama da shi.

Indiya ita ce ta biyu a duniya  ma fi yawan jama’a kuma tana bukatar man fetur daga wasu kasashe don warware matsalar makamashi da take fama da ita a halin yanzu.

Shugaban ya ce Nijeriya za ta ci gaba da tallafawa Indiya wurin warware matsalar da take fama da ita ta kowacce hanya da za ta iya.

Kyari ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a lokacin da wakilin Indiya, Abhay Thakur ya kai ziyara a hedikwatar NNPC a Babban Birnin Tarayyar Abuja.

Shugaban ya ci gaba da cewa, yarjejeniyar fahimatar juna da kasar nan ta kulla da Indiya suka rattaba hannu a kai za ta karfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da Indiyan.

Kyari ya kara da cewa, ce NNPC a shirye yake don yin hadaka  da Indiya don ganin kasashen biyu sun amfana da juna.

A cewarsa, “A shirye muke mu zauna tare da tawagar ‘yan kasuwa na Indiya don kasahen biyu su amfana.

A nasa jawabin, wakilin Indiya ya mika godiyarsa ga mahukuntan NNPC kan sabunta kwangilar samar da man fetur da aka ba wa kamfanonin Indiya uku damar shiga.

Mista Abhay ya bukaci Nijeriya ta kara adadin danyen man fetur din da za ta rika sayarwa Indiya domin samun damar warware matsalar da suka fama da ita
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: