Connect with us

RAHOTANNI

Yadda Ta Kaya Tsakanin Ashiru Da El-Rufa’i A Kotu

Published

on

A ranar Alhamis da ta gabata ne, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), a Jihar Kaduna, ta gabatar da shaida guda wanda daga nan ta rufe jawabinta a karar zaben Gwamnan Jihar da ke gaban kotun musamman mai sauraron kararrakin zaben.

INEC, wacce ita ce ta farko da ake kara a cikin karar da jam’iyyar PDP ta kai kotun, tun da farko ta gabatar da shaidu guda 10 ne wadanda suke kare ta.

Jam’iyyar ta PDP da dan takaranta na gwamna a zaben na ranar 9 ga watan Maris, Alhaji Isa Ashiru, suna kalubalantar sake zaben gwamna Nasiru EliRufai  na jam’iyyar APC ne a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kotun musamman din wacce ke karkashin mai shari’a Ibrahim Bako, a ranar 15 ga watan Yuli, ta dage sauraron bude kare kan na hukumar ta INEC ne zuwa ranar Alhamis, bayan ta kasa yin hakan a ranar Litinin.

Masu shigar da karan sun kulle na su maganar ne bayan sun gabatar da shaidu 135 domin tabbatar da tuhumomin da suke yin a tafka magudi, satan kuri’u da aukar da rigingimu  a lokacin zaben.

A lokacin hukumar ta INEC ta ce, za ta gabatar da shaidu guda 10 domin su kare ta, sa’ilin da guda Tara duk ma’aikatan hukumar zaben ne.

Sai dai a ranar Litinin, Lauyan hukumar zaben, Mista Aliyu Umar (SAN), ya sanar da kotun cewa, ba za su bude na su maganar ba, domin yawancin shaidun na su suna halartar taro a kan zaben ne a Abuja, sai ya nemi kotun da ta ba su zuwa ranar Alhamis, 18 ga watan Yuli, domin ta gabatar da nata maganar.

Bako ya amince da bukatar na su, ya dage sauraron zuwa ranar 18 ga watan na Yuli, domin hukumar zaben ta kawo shaidunta ta kuma gama rufe nata maganar a ranar ta Juma’a, 19 ga watan Yuli.

Sai dai kuma a lokacin da kotun ta dawo zaman nata a ranar Alhamis, INEC ta bude nata maganar ne da gabatar da tulin takardun da aka yi amfani da su a zaben na ranar 9 ga watan na Maris.

Daga baya ne kuma hukumar ta gabatar da shaida guda daya, Malam Ibrahim Umar, mataimakin daraktan ayyuka na hukumar zaben a Jihar, ta kuma kulle maganar nata bayan an yi masa tambayoyi.

Jagoran Lauyoyin ya shaidawa manema labarai a lokacin da suke tattaunawa da shi cewa, tulin takardun da kuma shaidar guda daya da suka gabatar sun isa wajen kare kan na su.

Umar ya ce, shaidar wanda masu karan suka yi masa tambayoyi ya bayar da amsoshin da suka gamsar da yawancin matsalolin da masu karan suke tuhuma a kai.

Sai dai kuma, kotun ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga watan Yuli, domin wanda ake tuhuma na 2 Gwamna Nasiru El-Rufai ya fara kare kansa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!