Connect with us

LABARAI

Jami’ar Jihar Ekiti Ta Yaye Likitoci Karon Farko Bayan Tsawon Shekara 10

Published

on

An saki sakamakon jarabawar karshe da daliban da ke karatun zama likita a jami’ar jihar Ekiti

Hakan ta faru ne bayana daliban sun kwashe tsahon shekaru 10 a jami’ar bisa tsaikon da jami’ar ta samu kafin hukumar likitoci kasa wato ‘Medical and Dental Council of Nigeria’ ta sahale musu.

A wata sanarwa da daraktan yada labaran jami’ar, Bode Olofinmuagun, ya sanar a ranar Lahadi ya ce an yaye daliban ne bayan ziyarar da hukunmar likitoci ta kasa ka kawo wa  makarantar a kwanannan inda ta sahale wa makarantar koyar da darasin.

Olofinmuagun ya ce, ‘sakamakon jarabawar da aka saki ya nuna cewa kasha 100 na daliban sun yi nasara a jarabawar. Dukkan dalibai 44 da suka rubuta jarabawar sun lashe jarabawar.

A cewar shi shugaban jami’ar na rikon kwarya, farfesa Olubunmi Ajayi, ya taya likitocin da jami’ar ta fara yaye wa murna.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!