Connect with us

LABARAI

Maniyyatan Gwambe 560 Sun Isa Kasa Mai Tsarki

Published

on

Maniyyata hajjin bana daga jihar Gwambe su 560 sun bar filin jirgin sama na Lawanti International Airport dake Gwambe zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

Sakataren gudanarwar da hukumar aikin hajji ta jihar, Alhaji Sa’adu Hassan, ya shaidawa manema labarai cewa; maniyyatan za su isa birnin Madinah ne inda tuni hukumar ta shirya musu wuraren saukarsu. A cewarsa tawaga ta biyu ta maniyyatan za su tashi ne a ranar Alhamis 25 ga watan Yuli.

Ya baiwa maniyyatan hajjin da suka ragu hakuri, inda ya ce su ci gaba da kasancewa cikin shiri domin koyaushe za a iya nemansu.

Alhaji Abubakar Shehu-Abubakar, Sarkin Gwambe kuma Amirul Hajj na jihar, ya nemi maniyyata aikin hajjin da su kasance masu bin doka da oda na kasa mai tsarki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa; maniyyata 1,460 daga jihar Gwambe ake sa ran za su gudanar da aikin hajjin bana.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!