Connect with us

WASANNI

Saura Kiris Gareth Bale Ya Bar Madrid, In Ji Zidane

Published

on

Alumu sun nuna  cewa kwanakin Gareth Bale a Real Madrid sun zo karshe bayan da akaji kocin kungiyar Zinedine Zidane ya ce kuingiyar  na iya bakin kokarin ta na ganin ta siyar da dan wasan.

Bale, mai shekaru 30, ya lashe kofin gasar nahiyar turai sau hudu tun zuwan sa kungiyar daga kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur a shekarar 2013 akan kudin Euro Miliyan 100 amma ya kasa samun gurbi doka wasa a kakar wasan da ta wuce.

Zidane ya sanar da manema labarai cewa ‘Baya cikin jerin ‘yan wasan da muka lissafa zasu doka wasan saboda muna kokarin siyar da shi, hakan ne yasa bai buga wasan jiya ba.

‘Bari muga ko cinikin zai yi yu gobe ba. Muna fatan cinikin ya yiyuwu cikin gaggawa don jin dadin kowa.’

Kafafan labaran kasar Spaniya sun sako Bale a gaba bayan da ya kasa cike gurbin  Cristiano Ronaldo wanda ya bar kungiyar ya koma Juventus a shekarar da ta wuce.

Madrid ta kare a matsayi na uku a gasar La Liga kakar wasan da ta gabata inda Barcelona wadda ta lashe gasar ta bata ratar maki 19.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!