Connect with us

KASASHEN WAJE

‘Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Kai Ziyara A Kan Iyakar Kudancin Kasar

Published

on

Wuni guda bayan ya bada bahasi game da halin da ake ciki a kan iyakar Amurka gaban ‘yan majalisar dokokin, shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Homeland Security, ya kama hanyarsa zuwa kan iyakar Amurka da Medico a karo na hudu a cikin ‘yan makwanni.

Sai dai shugaban a wannan lokaci ya je kan iyakar ne tare da wata tawagar sanatoci, domin su ga irin yanayin da ake ciki a wurin.

‘Yan majalisar da suka hada da ‘yan Democrats 12 da wani dan independent daya, sun ziyarci iyakar dake McAllen a jihar Tedas inda ake yawan gudanar da harkoki da kuma sintirin jami’an tsaro, inda hukumomi suka tsare mutane dake kokarin shigowa kasar a cikin aikinsu.

Wata sanarwar da ofishin shugaban Democrats a majalisar dattawa Chuck Schumer ya fitar na cewa tawagar da isa da safiyar shekaran jiya Juma’a ne tare da shugaban hukumar tsaron cikin gida Kebin McAleenan domin bincike da duban iyakar tare da tantance halin da ake ciki a kan iyakar kudancin kasar.

Sanata Chuck Schumer ya ce tawagar ta ga wani matsuguni mai kyau a ziyarar wuni daya da ta kai wanda wata kungiyar taimako ta Katolika ke gudanar da ita.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!