Connect with us

LABARAI

Sojoji Da Kwastam Sun Hadu Don Kawo Karshen Kalubalen Tsaro A Kan Iyakokin Najeriya

Published

on

Rundunar Sojin kasar nan da kuma hukumar Kwastam sun yi alkawarin yin aiki a tare domin magance matsalolin tsaro a kan iyakokin kasar nan wanda wasu baragurbi suke kalubalantar kasar nan da su. Hakan yana cikin sanarwar da sassan tsaron biyu suka gabatar ne a wajen rufe bikin gwajin yanda ake yin amfani da makamai da kuma horaswa da jami’an Sojojin da na hukumar Kwastam din suka gudanar a tare, inda kimanin jami’ai 2,000 na shiyyar D na hukumar Kwastam din da ke shiyyar Bauci suka gudanar.

Da yake Magana a wajen rufe bikin, Kwamandan runduna ta 33 na Sojojin atilare, Manjo Janar MT Durowaiye, cewa ya yi, an gudanar da shirin a cikin nasara, domin ba a sami wani hadari a cikinsa bas am.

Ya ce horaswan wani sashe ne na aikin hadin kai da hukumomin biyu suke yin a taimaka wa kokarin da Sojojin Nijeriya ke yi na tabbatar da manufar gwamnatin tarayya ta kawo karshen rashin tsaro a cikin kasar nan.

Shi ma da yake Magana, babban Kwamandan runduna ta 3 ta Sojin Nijeriya da ke Jos, Manjo Janar Nuhu Angbazo, cewa ya yi, an gudanar da shirin ne domin taimaka wa jami’an hukumar ta Kwastam da horaswa ta yanda za su iya kalubalantar ayyukan ‘yan sumoga, wadanda ya ce a halin yanzun sun kware suna kuma amfani da makamai. Nuhu Angbazo, wanda Birgediya Janar M. Danmadami, ya wakilce shi, ya yi kira ga wadanda suka sami horon da su yi amfani da dubarun da aka koya masu wajen kare kan iyakokinmu da kuma kore ‘yan sumoga wadanda suke barazana ga tsaron kasar nan da kuma tattalin arzikin kaar mu.

A na shi jawabin, Kwamandan shiyya na shiyyar D na hukumar ta Kwastam, Kashim Ajiya, cewa ya yi hukumar ta su ta kuduri aniyar horar da jami’anta ne domin su kalubalanci matsalolin tsaro da ake fuskanta a kan iyakokinmu. Ajiya, wanda Kwanturolan hukumar ta Kwastam mai kula da Bauci da Gombe, Kla Hafiz, ya wakilce shi, ya ce, horas da jami’an hukumar ta Kwastam a kan yanda ake yin amfani da makamai zai taimaka wajen magance kalubalen tsaro da su ke fuskantar nahiyar yammacin Afrika, a dalilin ayyukan ’yan sumogal makamai da sauran kayayyaki masu hadari.

Da yake Magana a kan yanda horaswan ta gudana, babban jami’in horaswan, Manjo L.T Madugu, cewa ya yi, horaswan an gudanar da shi ne kashi-kashi. A cewar shi, an shirya horaswan ne ga jami’an hukumar ta Kwastam guda 2000 a matakai daban-daban. Amma saboda wasu dalilai sun iya horas da jami’ai 1,718 ne kadai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!