Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Edo: An Halaka ’Yan Fashi Da Makami Guda Biyu

Published

on

A ranar Litinin ce, a ka halaka wasu mutum biyu wadanda a ke kyautata zaton ‘yan fashi da makami ne, lokacin da su ka je yin fashi a garin Benin babbar birnin Jihar Edo. An bayyana cewa, an kashe wadanda a ke zargin ne a yankin Ekehuan kusa da Asoro Hill, lokacin da su ke kokarin yin fashi. An kuma bayyana cewa, wani daga cikin tawagar ‘yan fashin mai suna Junior ya gudu da rauni a jikinsa. Lokacin da ‘yan fashin su ka isa yankin domin yin fashi, sai wasu daga cikin mazauna yankin su ka kira ‘yan sanda, inda ‘yan sanda su ka isa wurin da gaggawa, sannan su ka fatattaki ‘yan fashin da harbin bindiga.

Kwamishinan ‘yan sandar jihar, DanMallam Muhammed, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin. Ya bayyana cewa, “gaskiya ne an halaka ‘yan fashi da makami guda biyu a wani samame  da ‘yan sanda su ka kai, inda ‘yan sanda su ka kwato bindigogi tare da harsasai. “’Yan sanda sun samu kiran wayar salula, inda nan take su ka amsa kira tare da samun ‘yan fashin. Lokacin da ‘yan fashi su ka hangi ‘yan sanda, sai su ka fara harbe-harbe, inda ‘yan sanda nan take su ka maida martani, ‘yan sanda sun fatattake su.”

Kwamishinan ‘yan sanda ya bukaci mutane da su cigaba da bai wa ‘yan sanda hadin kai wajen dakile ayyukan ta’addanci a cikin jihar baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!