Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Inugu: ’Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Dalibin Da Ya Kashe Kansa

Published

on

Kwamishinan ‘yan sandar Jihar Inugu, Mista Sulaiman Balarabe, ya bayar da umurnin gudanar da bincike a kan zargin da ake yi na cewa, wani dalibin jami’ar Nsukka mai suna Chukwuemeka Ugwuoke ya kashe kansa. Kakakin rundunar ‘yan sandar jiha, SP Ebere Amaraizu, shi ya bayyana hakan ne ga kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a garin Inugu ranar Asabar. Amaraizu ya bayyana cewa, lamarin ya afku ne a ranar 13 ga watan Mayu. Ya kara da cewa, kwamishina ‘yan sandar jihar ya bai wa sashin rundunar ‘yan sanda masu binciken manyan laifuka umurnin gudanar da cikakken binciken yadda a ka yi dalbin ya kashe kansa.

Ya ce, shi dai Ugwuoke mai shekaru 21 da haihuwa, ya na karatu a jami’ar Nsukka, inda ya ke karanta hashe turanci, shi dai dalibin dan asalin kauye Amodoloro Umuabor da ke garin Eha Alumona cikin karamar hukumar Nsukka ta jihar.

“Ana zargin cewa dalibin ya shiga wani kango a cikn jami’a rana 13 ga watan Mayu, inda a ke zargin ya sha maganin kwari mai suna ‘Snipper’ har kwalba guda biyu.

“Bayan ya sha wannan maganin, sai ya kira abokinsa a wayar salula inda ya bayyana masa cewa shi ya sha maganin kwari, nan take abokin nasa ya isa wurin, inda ya ganshi ya na ta haki daga baya kuma ya mace.

“An garzaya da shi zuwa dakin shan magani na jami’ar Nsukka, amma daga baya an mika shi zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Nsukka da ke yankin Ituku Ozalla inda a nan ne likita ya tabbatar da mutuwarsa.”

Amaraizu ya cigaba da cewa, wannan shi ne karo na hudu da dalibai su ke yin yunkurin kashe kansu a wannan jami’ar, ya na zargn cewa duk daliban da suka kashe kan su din, su na fama da matsalar rayuwa ne.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!