Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Jigawa: Wasu Manoma Biyu Sun Nutse A Cikin Kogi A Kauyen Kazuba

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Jigawa ta bayyana cewa, wasu manona guda biyu sun rasa rayukansu, lokacin da su ka yi yunkurin tsallake wani kogi a kauyen Kazuba da ke cikin karamar hukumar Kiyawa ta jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar, SP Abdu Jinjiri, shi ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a garin Dutse.

Ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne ranar 20 ga watan Yulin shekarar 2019 da misalin karfe 4.20 na yamma. Ya kara da cewa, sun samu rahoton lamari ne a ofishin ‘yan sandar karamar hukumar Kiyawa cewa, wasu manoma guda biyu sun nutse a cikin kogi, lokacin da su ke kokarin tsallaka ruwan domin zuwa gonarsu.

Jinjiri ya ce, a cikin wadanda su ka rasa rayukansu har da Rabiu Abubakar dan shekara 30, dan asalin kauyen Kagadama da kuma Adamu Sa’idu mai shekaru 35, dan asalin kauyen Kazuba da ke cikin karamar hukumar Kiyawa. Ya ce, Rabi’u Abubakar ya mutu ne a wannan rana lokacin da mazauna yankin su ka tsamo shi. Jinjiri ya kara da cewa, Adamu Sa’idu, an gano gawar shi ne a cikin kogin a ranar 21 ga watan Yulin shekarar  2019 da misalin karfe 12.30 na rana. Ya kuma bayyana cewa, dukkan mamatan an tabbatar da mutuwarsu ne tab akin likitan babban asibitin Kiyawa. Ya bayyana cewa, an mika gawarwakin mamatan ga iyalansu, sannan har ma an mu su jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ta tanada. Jinjiri ya gargadi manoma da su dunga kulawa a duk lokacin da su ka zo tsallake kogin musammam ma a wannan lokacin da ruwa ya yi yawa, sakamakon ruwan sama da a ke yi kamar dab akin kwarya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!