Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Osun: An Gurfanar Da Wani A Kotu Bisa Satar Babur Din Lauya

Published

on

A ranar Litinin ce, a ka gurfanar da wani mutum mai suna Tajudeen Kazeem dan shekara 34 da haihuwa, a gaban kotun Jihar Osun wacce ta ke da zama a garin Osogbo, bisa laifin satar babur guda biyu. Daya daga cikin baburan kirar Jincheng mai lamba kamar haka KC 111 EJG, Wanda kudinta ya kai naira 55,000, mallakar wani lauya ne mai suna Mustapha Abdulfatai. Wanda a ke tuhuma ana zargin ya sace babur din ne daga gidan lauya mai lamba 13 da ke kan titin Orisumbare cikin yankin Oke-Bale cikin garin Osogbo, a ranar 7 ga watan Afrilun shekarar 2019 da misalin karfe 11 na dare.

Ana kuma tuhumar Kazeem da sace babur kirar Hauojue Suzuki mai lamba kamar haka KH 639 SBG, wanda kudinta ya kai naira 65,000, mallakar wani mutum mai suna Salawu Kamorudeen. Ya canza lambar babur din zuwa KC 111 EJG. An dai gurfanar da Kazeem ne tare da wani mutum mai suna Adamoh Raji, wanda ya sayi babur din da ya sato kirar Hauojue Suzuki daga hannunsa.

Wadanda a ke tuhuma sun musanta dukkan laifukan da a ke tuhumar su guda biyar.

Lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kara, ASP Abiodun Fagboyinbo, ya bayyana cewa, wannan laifin dai ya saba wa sashe na 508, 427 da kuma 390 (4) (c), wanda ya ke da hukunci a sashe na 509 a cikin dokar manyan laifuka mai lamba Cap 34, Bol II, ta Jihar Osun ta shekarar 2003.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: