Connect with us

SIYASA

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan kisan kananan yara a Nijeriya

Published

on

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da hare-haren ta’addanci da ake kai wa kan yara kanana a yankin Maiduguri da ke yankin Arewa maso gabashin Nijeriya. Kai harin ta’addanci kan farafren hula babban abin tashin hankali ne.

Harin da yayi sanadiyar asarar sama da mutum 30 cikin su harda yara kanana . Kauyen Mandarari yanada nisan kilomita 40 tsakanin sa da babban birnin Maiduguri.

Da yake nuna alheninsa da muryan Majalisar Dinkin Duniya Mista  Edward Kallon yace ; yan ta’adda basu da tausayi basu da imani saboda suna kisan fararen hula wadanda basun hawaba bare sauka.

Yace; yara kanana suna da rawar da zasu taka na cigaban kasa amma haka kawai , ake kai hari ana kashe su ba tare da nuna tausayi ba.

Ya kara da cewa Mata da suke gudanar da ayyukan jinkai suma basu tsira ba daga yadda yan ta’addan ke kashe su ko su kwashesu zuwa daji domin yimasu aikin bauta.

Ya ce ; yanzu haka al’umman da suke cikin halin jinya suna bukatar magani  a Asibiti.

Ana kai hare hare guraren da farafren hula ke haduwa su gudanar da ayyukan su na cigaba kamar kasuwa da filayen wasannin.

Idan mutum yana kallon ire iren wannan ko a akwatin talabijin abin yakan bada tausayi.

Wasu kaga an raunatasu da bama bamai ko harsasai. Ya ce; a shekarar 2018 an samu asarar rayuka yara kanana 289 wadanda harin ta’addanci ya kashe.

Yace; Majalisar Dinkin Duniya tana nuna matukar damuwa da irin zaman kunci da Iyaye mata suke kasancewa a sansanonin ‘yan gudun hijira sakamakon yadda harin  Ta’addanci ke  rabasu da muhalinsu
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: