Connect with us

SIYASA

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kagara Ya Bayyana Aniyarsa Na Yin Takara Karo Na Biyu

Published

on

Tsohon shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa, Hon. Tanko Bojoh ya bayyana aniyarsa na yin takarar shugabancin karamar hukumar Rafi karo na biyu. Bojoh ya bayyana wannan kudurin ne a lokacin da ziyarci sakatariyar jam’iyyar APC na karamar hukumar Rafi da ke Kagara laraban makon nan mai karewa.

Ya bayyana wa shugaban jam’iyyar cewar ya shugabanci karamar hukumar Rafi tsawon shekaru uku kuma kowa shaida ne akan irin ci gaban da ya kawo a karamar hukumar Rafi wanda an samar da tsaftataccen ruwan sha da kuma tallafawa rayuwar matasa ‘yan boko da ‘yan kasuwa, wanda idan ya samu goyon baya wajen samun nasarar dawo wa zasu cigaba da bada shugabancin mai adalci ga mutanen Rafi musamman ganin irin wannan lokacin da tsaro ya zama barazana ga al’ummar Rafi.

Hon. Bojoh ya nemi jam’iyyar APC da ta ba shi dama wajen ganin ya samu nasarar takarar da za ta baiwa jam’iyyar daman sake darewa kan shugabancin karamar hukumar. Yanzu haka kiraye-kirayen iyayen mu mata da matasa ya sa ke ba mu kwarin gwiwar sa ke neman wannan matsayin karo na biyu domin sun gamsu da irin shugabancin da muka yi na shekaru uku a baya.

Sanin kowa ne kasar Rafi ta shahara akan noma da kasuwanci, za mu hada hannu da ‘yan bokon mu da ‘yan siyasa dan ganin gwamnatin jiha da ta tarayya sun samar da abubuwan da zai kara daga darajar noma da kasuwanci a karamar hukumar ta yadda har wadanda ba su samu damar yin karatu mai zurfi ba cin moriyar ayyukan cigaban kasa na gwamnati ta hanyar dogaro da kai da magance matsalolin ‘yan ta’adda da ke damun al’ummar mu.

Tsohon shugaban dai bayan barin sa sakatariyar jam’iyyar ya ziyarci fadar mai martaba sarkin Kagara, Alhaji Salihu Tanko don bayyana aniyarsa na yin takarar da kuma nan albarka.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: