Connect with us

LABARAI

Wata mata ta Dabawa Mijinta Wuka A Kaduna

Published

on

Sakamakon sabanin day a shiga tsakanin wata mata mai suna A’isha jiya Juma’a tare da mijinta mai suna, Yahaya Maiyaki ta daba masa wuka har sau biyu a ciki. Suna zau ne tare da mijin nata a wata unguwa da ake kira Sarduana Crescent. Majiyarmu ta shaida mana cewa, sun fara samun sabanin tun cikin dare.

Kamar yadda dan uwan mijin matar ya fada, “A’isha ta yi kokarin kona shi da ruwan zafi tun a cikin daren, amma bat a samu sa’a ba, saboda haka sai ta jefe shi da tukunyar rowan zafin. Da ta ga ba ta same shi ba, sai ta dauko wuka ta daba masa a ciki.”

Majiyarmu ta shaida mana cewa yanzu haka mijin na nan kwance a  asibiti. “Abin mamakin shi ne yanzu shekararsu biyar da aure kuma suna da da daya. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da afkuwar wannan lamari, sannan kuma ya ce, suna nan suna yin bincike.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: