Connect with us

TATTAUNAWA

Mu Na Neman Taimakon Gwamnati A Kasuwar Fanteka – Garkuwan Matasa

Published

on

ALHAJI NURA HARUNA BABBA, GARKUWAN MATASAN TUDUN WADA KADUNA, shi ne zababben shugaban kasuwar sabuwar Fanteka da ke Kaduna, kasuwar da ta shahara a kan batun kayan mota manya da kanana. Kasuwar sabuwar Fanteka, ana jin ta a matsayin iyaka ce a kan maganar kayan mota ba a garin Kaduna, arewa ko ma kasar nan ba kadai, Kasuwa ce da har a ketaren kasar nan ake magananta, kusan duk abin da aka rasa na mota, in an zo sabuwar Fanteka za a same shi tamkar a nan ne ake kera shi. A zantawan da Garkuwan na matasa ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke kasuwar, ya yi magana ne a kan abin da ke ciwa kasuwar tuwo a kwarya wanda suke neman tallafin gwamnati a kansa, sannan ya yi bayni kadan a kan irin gudummawar da kasuwar ke bayarwa ta fannin tattalin arzikin kasa.

Wakilin LEADDERSHIP A YAU, UMAR A. HUNKUYI, ya halarci zaman. Ga abinda ya jiwo daga bakin shugaban kasuwar kai-tsaye. A sha karatu lafiya:

Muna yin kira gami da roko ba ga gwamnatin Jihar Kaduna kadai ba, har zuwa ga gwamnatin tarayya da duk ma wani dan majalisa na tarayya har zuwa na Jiha da su zo su dube mu, su kuma dubi ayyukan da muke yi domin mu diyansu ne. Muna bukatar taimako masu yawa, a yanda muke kokari muna ta tallafan ‘ya’yanmu domin su nemi na kansu, ya kamata gwamnati ta zo ta duba mu, a ba mu jari, ko da kuwa ba a ba mu jarin nan kai tsaye ba, a nema mana hanyoyin da za mu rika samun kayayyakinmu da sauki, domin kaya ne da ake samo su daga kasashen waje. To zai yi kyau in har aka sama mana sauki mu da muke tafiya kasashen waje nemo kayan nan, ko da ta hanyar samun kudaden canjin nan kai tsaye ka ga duk wannan taimako ne.

Taimakon da gwamnati za ta yi mana a nan yana da yawa, amma wajibi ne gwamnatin ta turo wanda yake da ruwa da tsaki a kan wannan al’amarin ya zauna da mu ko a gayyace mu, duk da mun san al’amari na kasa abubuwan sun yi yawa, mun san dai ana sane watakila kuma ko an manta shi ya sanya a duk lokacin da na samu dama irin wannan nake kara tunatarwa ga gwamnatin ta zo kusa da mu ta ga me muke yi.

Musamman a kan maganar hasken lantarki da muke da tsananin bukata a cikin wannan kasuwa, na yi ta rubuce-rubuce ba iyaka, muna da tabbacin in har da muna da hasken lantarki a cikin wannan kasuwar da mun fi haka a halin yanzun, rashin hasken lantarjkin nan ba karamin nakasu ne yake kawo mana ba a cikin wannan kasuwar. Ya kamata gwamnati ta dubi Allah ta taimaka mana, musamman dai batun hasken lantarkin nan da kuma hanyar da ke cikin kasuwar nan. Muna kuma fa biyan duk kudaden harajinmu, ba a samun mu da wata matsala ta rashin samar da kudin shiga ga gwamnati a wannan kasuwar, muna biyan haraji a kowane lokaci, don haka ya kamata gwamnati ta taimaka a duba mana wadannan matsaloli, muna kuma godiya sosai ba domin gwamnatin ta gaza ba, sai domin dai kara janyo hankalinta kadai.

Sau da yawa wasu sukan kasa bambancewa a tsakanin ita wannan kasuwa ta mu ta sabuwar Fanteka da kuma tsohuwar Fanteka. A baya can kasuwar Fanteka duk a hade ne take, amma a sabili da yawan cinkoso ne aka zo a zamanin wani gwamnan mulkin Soja aka raba mu, a shekarar 1985 mu aka rabo mu daga waccan Fantekan musamman mu masu hulda na kayayyakin mota, aka dawo da mu a nan. A takaice dai Fantekokin biyu tamkar Ya ce da kanwa, waccan ce Yar, mu ne kanwa. Su a waccan Fantekan suna hulda ne da kayayyakin gine-gine da abubuwan yanayi na gida, kayan walda da makamantansu. A yanzun haka wannan kasuwar ta mu ta sabuwar Fanteka tana da kimanin shekaru 36 kenan, ni ne kuma zababben shugabanta na biyu a hanyar zabe na siyasa, a baya nadi ne kawai ake yi.

Baya ga harkar kasuwanci da muke yi a cikin wannan kasuwa, muna kuma yin ayyukan da suka shafi kere-kere, inda muke janyo matasa muna koya masu, wanda idan ka kewaya cikin kasuwar Fanteka za ka ga hakanan. Sabanin a baya, da ka ambaci sunan Fanteka inda ake siyar da kayan mota, sai a ce maka ai Inyamurai ne. To a halin yanzun ga mu Hausawa mun shigo ciki har mun goge ga shi yau kasuwar siyar da kayan motar ma Bahaushe ne yake shugabancin ta, ka ga an samu ci gaba sosai.

A halin yanzun haka, in aka nemi kayan mota aka rasa, in dai an zo mana da samfurinsa to a bisa kwarewar da jama’armu a nan suke da shi za su iya kera maka wannan abin har ma ya fi wand aka zo mana da shi karko, ko kamar a ce rim din mota ya fashe muna da wadanda za su kera su mayar da shi har ma ya fi na da, da dai makamantan hakan.

A baya kasuwar Fanteka ba haka take ba, a yanzun kasuwar Fanteka ta zama kasuwa ce ta Afrika in dai a kan maganar kayan mota ne. Da yawa abin da za a karade ana nema a rasa, amma in aka zo nan za a same shi. A yanzun muna da alaka da kasuwanni na Duniya, sun sanmu, mun san su. Akwai kuma matasanmu a nan da mukan taimaka wa domin ba ma son mu ga mutum yana zaune haka kawai, musamman mata masu siyar da abinci wadanda wala’alla ko jarin su ne ya karye ko muka lura suna cikin matsala, lallai kungiyar sabuwar Fanteka a karkashin Alhaji Nura Haruna Babba, muna dan ba su tallafi.

Mu na kuma janyo samarin nan namu a jiki saboda yanayin yadda rayuwa take a halin yanzun, yanda yara suka baci da shaye-shaye da makamantan hakan. To muna sa wa ana lura da su, muna da ‘yan sanda na ciki wadanda suke a karkashin kasuwar Fanteka muna sa wa suna lura mana da irin wannan.

Babban kalubalen da muke fuskanta, a baya idan aka ce kasuwar Fanteka sai a dauka ai duk barayi ne ma a cikinta, ka zo da motarka ta bace ko ka zo da mashin dinka ya bace. A yanzun haka, kasuwar sabuwar Fanteka a karkashin mulki na, a baya mutum in ya je ya siyo mota tsakaninsa da mai mota ne, amma yanzun in ka je ka siyo mota, to kafin ma ka fara komai tilas ne sai mun ga takardun motar nan sun cika sun kuma shiga cikin rajistanmu.

Tabbas duk wanda ya zo mana nan akwai bincike da sauran su, in ma ka zo ka fara kwance motar, su wadannan masu binciken suna nan suna yawo za ka gansu da kayan aikin su da muka dinka masu. Har in ka karya doka ka fara aiki ba tare da sun zo sun tantance motar naka ba, akwai hukunci, wanda a lokacin kuma mu sanya maka bincike mai tsanani, in har mu ka kama cewa motar naka ba ta gaskiya ce ba ko ba ta cika ka’idar da ya kamata ba, to mu na da alaka da ‘yan sanda sai mu tura masu maganarka su je su bincika.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: